Sunday, July 5
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Hotuna: Rahama Sadau ta saki Hotunan Murnar zuwan watan Ramadan

Kalli Hotuna: Rahama Sadau ta saki Hotunan Murnar zuwan watan Ramadan

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata data saka a shafinta na sada zumunta tanawa masoyanta barka da zuwan watan Ramadana.
Jihohin Katsina da Bauchi sun bayar da hutun Azumin Watan Ramadan ga ‘yan makaranta

Jihohin Katsina da Bauchi sun bayar da hutun Azumin Watan Ramadan ga ‘yan makaranta

Duk Labarai
Jihohin Bauchi da Katsina sun bayar da hutun Watan Azumin Ramadana ga 'yan makaranta. A jihar katsina, bayan kulle makarantun Gwamnati, Hukumar HISBAH ta jihar ta kuma fitar da sanarwa ga masu marantu masu zaman kansu dasu kulle makarantun nasu har sai bayan Azumin watan Ramadana. Kwamandan HISBAH na jihar, Aminu Usman ne ya fitar da sanarwar inda yace rashin yiwa wannan doka biyayya zai sa a hukunta duk makarantar da aka kama suna karatu. Hakanan a jihar Bauchi na, mahukuntan jihar sun bayar da hutu daga ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa ranar 5 ga watan Afrilu ga makarantu.
Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2025

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2025

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2025 da ya kama naira tiriliyan 54.99 Kasafin kuɗin na wannan shekara ya zarta na shekarar da ta gabata - wanda aka yi a kan naira tiriliyan 27.5 - da kashi 99.96 cikin 100. Shugaban ya sanya hannu kan kasafin ranar Juma'a a fadarsa da ke Abuja. An dai ƙara yawan kasafin na farko da shugaan ya aikewa majalisa na naira tiriliyan 49.7. A ranar 13 ga watan Fabrairun da muke ciki ne majalisar dokokin ƙasar ta amince da kasafin, bayan muhawara a kansa. An dai tsara kashe naira tiriliyan 14.32 wajen biyan bashi, inda manyan ayyuka za su laƙume naira tiriliyan 23.96.
Ya kamata a binciki Sanata Akpabio kan zargin làlàtà da Natasha Akpoti tai masa>>Inji Atiku

Ya kamata a binciki Sanata Akpabio kan zargin làlàtà da Natasha Akpoti tai masa>>Inji Atiku

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin majalisar dattijai da cewa ya kamata au binciki kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio kan zargin da Sanata Natasha Akpoti tai masa na son yin lalata da ita. Atiku a sanarwar da ya fitar ya nemi cewa a matsayin Akpabio na mutum na 3 wanda yafi karfin fada aji a Najeriya, ya kamata ace yana da mutunci da tsare kai da tarbiyya. Atiku yace ya kamata a kafa kwamiti na musamman me zaman kansa da zai binciki sanata Akpabio kan wannan zargi. Atiku yace wannan lamari zai sa Duniya ta fahimci irin tsarin Adalci da Najeriya ke da shi.
Yanda Sanata Akpabio Ya taba rike hannuna a gaban mijina>>Sanata Natasha Akpoti

Yanda Sanata Akpabio Ya taba rike hannuna a gaban mijina>>Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi ta bayar da labarin yanda Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya taba rike hannunta a gaban mijinta. Tace a lokacin sun je taya Akpabio murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne inda mijinta ya rakata. Tace Sanata Akpabio ya kama hannunta ya jata ya rika nuna mata gidansa yayin da mijinta ke binsu a baya. Tace abin ya damu mijinta a lokacin wanda daga nan ya rika cewa ba zata rika yin tafiya ita kadai ba.
GWAMNATIN JIHAR KEBBI TA AURARDA ‘YA’YA MATA 300 (DA MAZAJENSU) KARO NA 2 !

GWAMNATIN JIHAR KEBBI TA AURARDA ‘YA’YA MATA 300 (DA MAZAJENSU) KARO NA 2 !

Duk Labarai
A jiya Alhamis ne (27/02/2025) Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin zababben Gwamnan Jihar (Comr. Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu) ta sake daurawa mata 300 aure da mazajensu , tareda duk abinda ya dace ayi musu na karramawa (auren gata kenan). Wannan kudurin (na shirin auren gata) mai girma Gwamnan Jihar Kebbi ya sanya shi a ransa , cewa da ikon Allah zai yi iya na shi kokari don ganin gwamnatinsa ta ci gaba da bada irin wannan gudummuwa musamman ga marasa karfi , don taimakawa al'umma wajen rage yawan gwagware da kuma rage yaduwar alfasha a cikin al'umma. Ko shakka babu wannan ba karamin alkhairi bane a cikin al'umma musamman idan sun gano hadarin da ke cikin yawaitar mabukata aure mata/maza kuma ba suda halin yin auren , a irin wannan lokacin komai na iya faruwa a kowane bangar...
Tonon Silili: Dama can Sanata Akpabio da Natasha Akpoti sun san juna kamin ta zama sanata>>Inji Daya daga cikin sanatocin

Tonon Silili: Dama can Sanata Akpabio da Natasha Akpoti sun san juna kamin ta zama sanata>>Inji Daya daga cikin sanatocin

Duk Labarai
Sanata me wakiltar Birnin Tarayya, Ireti Kingibe ta bayyana cewa dama can sanata Natasha Akpoti da kakakin majalisar, Godswill Akpabio sun san juna kuma akwai wani abu a tsakaninsu kamin ta zama sanata. Ta bayyana hakane a yayin da sanata Natasha Akpoti ta fito ta zargi kakakin majalisar da cewa ya nemeta da lalata ne ta ki shiyasa ya canja mata gurin zama a majalisar kuma yake dakile kudirorin da take kawowa. Sanata Ireti Kingibe ta bayyana cewa, ba Sanata Natasha Akpoti kadai bace aka canjawa wajan zama a ranar ba. Ta jawo hankalin cewa hakan tsari ne na majalisar wanda kuma duk dan majalisar ya kamata yana girmama hakan.
Da Duminsa:An dauke wutar Lantarki a fadar shugaban kasa, Tinubu

Da Duminsa:An dauke wutar Lantarki a fadar shugaban kasa, Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni daga fadar shugaban Najeriya dake Abuja sun bayyana cewa an samu daukewar wutar lantarki. Matsalar wutar lantarkin ta farune a wasu sassan na Abuja wanda har ta kai ga lamarin ya taba fadar shugaban kasar. Hukumar wutar lantarki ta Abuja, (AEDC) ta tabbatar da hakan a shafinta na X inda ta baiwa masu hulda da ita hakuri da kuma tabbacin cewa injiniyoyinta na aiki tukuru dan shawo kan matsalar. Karin guraren da matsalar wutar lantarkin suka shafa sun hada da Lugbe da Kubwa.
MASHA ALLAH: Kalli Hotunan Yadda Aka Kawata Masallacin Sheik Yusuf Guruntum Domin Fuskantar Tafsirin Watan Ramadan.

MASHA ALLAH: Kalli Hotunan Yadda Aka Kawata Masallacin Sheik Yusuf Guruntum Domin Fuskantar Tafsirin Watan Ramadan.

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} MASHA ALLAH: Yadda Aka Kawata Masallacin Sheik Yusuf Guruntum Domin Fuskantar Tafsirin Watan Ramadan.