Tsaka Mai wuya: Da wuya Osimhen ya bugawa Napoli wasa a wannan shekarar
Rikicin dan wasan Najeriya, Victor Osimhen da kungiyarsa ta Napoli ya kara kamari inda a yanzu babu tabbacin zai bugawa kubgiyar wasa a wannan kakar duk da yake cewa har yanzu yana kungiyar bai samu tafiya Chelsea kamar yanda ya so ba.
Osimhen dai yaki yin atisaye da kungiyar da tunanin cewa zai barta amma sai ciniki bai kaya ba na komawa Chelsea.
Hakanan kungiyar Napoli ta buga wasanta na farko da Parma kuma ba'a ga Osimhen a ciki ba wanda dama bai buga wasannin Preseason ba.
Kungiyar ta Napoli dai tuni ta baiwa Remolu Lukaku lamba 9 da Victor Osimhen ke goyawa.
A yanzu dai an dakatar da Osimhen daga duka wasanni da atisayen kungiyar ta Napoli kuma bai san makomarsa ba.