YANZU-YANZU: Gwamnatin Tinubu ta fara sayar da buhun shinkafa a kan farashin dubu Arba’in N40,000
Gwamnatin tarayya ta fara siyar da metric ton 30,000 na nikakken shinkafa ga al'ummar Najeriya akan farashin naira n40,000 akan kowanne buhu mai nauyin kilo 50.
A ranar Alhamis ne a Abuja Ministan Noma, Abubakar Kyari ne ya kaddamar da rabon tallafin shinkafar kan wannan farashin.
Shin ko shinkafar tazo gare ku a halin yanzu ?