Friday, July 3
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Jam’iyyar ADC ka iya samun Tangarda: Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta cire Shugaban ADC na rikon kwarya da sakataren jam’iyyar na Rikon Kwarya daga shafinta

Jam’iyyar ADC ka iya samun Tangarda: Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta cire Shugaban ADC na rikon kwarya da sakataren jam’iyyar na Rikon Kwarya daga shafinta

Duk Labarai
Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta sanar da cire shugaban jam'iyyar ADC na rikon kwarya, David Umahi da sakataren jam'iyyar na rikon kwarya, Rauf Aregbesola daga shafinta na tattara bayanan shuwagabannin jam'iyyun Najeriya. INEC tace ta yi hakanne saboda karar da aka shigar a kotun daukaka kara daga wani bangare na jam'iyyar da basu yadda da shugabancin su David Mark ba. Kwamishinan yada labarai na INEC, Mohammed Kudu Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yace zasu dakata har sai sun ji hukuncin da kotun daukaka karar zata yanke. Wanda ya shigar da karar shine Nafiu Bala Gombe wanda ke ikirarin cewa shine shugaban jam'iyyar ta ADC.
Hukumomi sun kori baturen kasar Amurka da ya shigo Najeriya yake tunzura Kiristoci akan Musulmai

Hukumomi sun kori baturen kasar Amurka da ya shigo Najeriya yake tunzura Kiristoci akan Musulmai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumomin Najeriya sun kori dan kasar Amirkar nan me suna Mr. Alex Barbir wanda ya shigo Najeriya yake tunxura Kiristoci akan Musulmai. Malam Bashir Ahmad wanda tsohon Hadimin shugaban kasa ne ya bayyana hakan ta shafisa na X inda yace wata majiya me karfi ta sanar dashi hakan. https://twitter.com/i/status/2039371038832603359 A baya dai, an yi kiran Hukumomin su dauki mataki akan wannan bature da ba'a amince da salon da ya shigo dashi Najeriya ba.
Mutanen da kuka gani a wajan komawar Kwankwaso ADC kudi aka basu ba soyayyar gaskiyace ba>>Inji Gwamnatin Abba

Mutanen da kuka gani a wajan komawar Kwankwaso ADC kudi aka basu ba soyayyar gaskiyace ba>>Inji Gwamnatin Abba

Duk Labarai
Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa dubban mutanen da suka taru a wajan komawar Rabiu Musa Kwankwaso Jam'iyyar ADC kudi aka basu. Kwamishinan yada labarai na Kano, Ibrahim Waiya ne ya bayyana haka a ganawarsa da AIT. Yace sun san yanda ake yi, idan za'a yi taro ana bi kauyuka akwai wadanda ake baiwa kudi su rika tara maka mutane. Yace a yanzu Abba ya shiga siyasar kasa inda yake damawa da sauran takwarorinsa.
Daga yau Karku kara jiran Umarni, duk inda kuka ga Tshàgyèràn Dhàjì ku Shèkyèshi kawai>>Ministan Tsaro, Christopher Musa ya baiwa sojoji Umarni

Daga yau Karku kara jiran Umarni, duk inda kuka ga Tshàgyèràn Dhàjì ku Shèkyèshi kawai>>Ministan Tsaro, Christopher Musa ya baiwa sojoji Umarni

Duk Labarai
Ministan tsaro, Christopher Musa ya baiwa sojojin Najeriya umarnin kada su sake sauraren umarni, duk inda suka ga dan Bìndìgà su aikashi kiyama. Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai rundunar operations hadin kai dake Maiduguri. Ko sa a baya lokacin yana shugaban sojojin Najeriya, Christopher Musa ya taba bayar da irin wannan umarni wanda ya jawo masa yabo sosai.
Rahoton sun bayyana cewa shugaba Tinubu na shirin sauke Malam Nuhu Ribadu daga Mukamin me bashi shawara kan harkar tsaro

Rahoton sun bayyana cewa shugaba Tinubu na shirin sauke Malam Nuhu Ribadu daga Mukamin me bashi shawara kan harkar tsaro

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin sauke Malam Nuhu Ribadu daga mukamin me bashi shawara akan harkar tsaro. Rahoton yace Malam Nuhu Ribadu na da shirin tsayawa takarar gwamna a jihar Adamawa, wanda na daya daga cikin dalilan saukar tasa. .Inda kuma a wani bangaren rahoton yace shugaba Tinubu na shirin yiwa harkar tsaro garambawul ne. Rahoton dai nata yawo ne a kafafen sada zumunta inda zuwa yanzu fadar shugaban kasa batace uffan akai ba.
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Bidiyoyin sabuwar Tqrzhomqr data barke a Garin Jos Jihar Filato sun dauki hankulan mutane sosai

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Bidiyoyin sabuwar Tqrzhomqr data barke a Garin Jos Jihar Filato sun dauki hankulan mutane sosai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa sabuwar Tqrzomq ta barke a birnin Jos na jihar Filato bayan da aka saukaka dokar hana zirga-zirga. An ga Bidiyon kala-kala na yawo a kafafen sada zumunta inda mutane ke guje-guje. A yayin da a wasu yankunan kuma aka ga jami'an tsaro na sintiri. https://twitter.com/i/status/2039324589503741999 https://twitter.com/i/status/2039329059688128946 https://twitter.com/i/status/2039286176381640875
Kalli Bidiyon: Matasa sun fito Zanga-zanga a jihar Edo inda suka ce kada wanda ya sake ya kawo musu shinkafar da shugaba Tinubu ke rabawa tallafi, basaso dan su ba mayunwata bane

Kalli Bidiyon: Matasa sun fito Zanga-zanga a jihar Edo inda suka ce kada wanda ya sake ya kawo musu shinkafar da shugaba Tinubu ke rabawa tallafi, basaso dan su ba mayunwata bane

Duk Labarai
Matasa a jihar Edo sun fito zanga-zanga inda suka ce basa son tallafin shinkafar da Gwamnatin tarayya ke rabawa. Sun bayyana cewa su ba shinkafa bace matsalar su, ta yaya, Duk wata matsala da ake da ita, shinkafa kawai za'a kawo? Matasan sun ce abin ya isa haka: https://twitter.com/i/status/2039286568280523130
Da Duminsa: An gama zaman Kotu ba tare da kotun ta bayar da belin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ba, Sannan ICPC sun Mikashi hannun DSS

Da Duminsa: An gama zaman Kotu ba tare da kotun ta bayar da belin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ba, Sannan ICPC sun Mikashi hannun DSS

Duk Labarai
Rahotanni daga babbar kotun tarayya dame Kaduna inda ake shari'ar tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sun bayyana cewa. Lauyoyin Tsohon gwamnan sun nemi a bayar da belinsa sannan suma Lauyoyin Gwamnati sun bayar da nasu bayanan. Bayan kammala sauraren kowanne bangare, Kotun tace ta saka ranar 14 ga watan Afrilu dan yanke hukunci kan shari'ar. Saidai wannan rana ta yi daidai da ranar babban taron jam'iyyar ADC na kasa, inda wasu ke zargin da gangan aka yi hakan. https://twitter.com/i/status/2039320096514925046
Wata Sabuwa: An kama Direban Matar sarkin Kano da zargin satar Gwal na Naira Miliyan sittin

Wata Sabuwa: An kama Direban Matar sarkin Kano da zargin satar Gwal na Naira Miliyan sittin

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, an gurfanar da direban matar me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da wasu mutane 2 a gaban kotun Magistrate dake Nomansland a Kano. Ana zarginsu ne da satar Gwal na Naira Miliyan 60 da kuma karbar kayan sata. Wadanda ake zargin sune Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa, da Abdullahi Usaini. Hakanan ana zarginsu da satar kudi da kuma wayar hannu. Yayin zaman kotun, Sulaiman ya amsa duka laifukan da akw zarginsu da aikatawa saidai sauran biyun da ake zargi sun musanta zargin da ake musu. Lauyan wadanda ake zargin, Barrister A.A. Abdullahi ya bukaci a bashi belin wadanda ake zargin inda mai shari'a, Magistrate Halilu Abdurahman ya bayar da belin da sharuda masu tsanani. Yace dole duk wanda zai karbi belinsu ya zamana ma'aikacin Gwamnati dake ...