Senator Chris Coons meeting with Bill Gates at the Russell Senate Office Building on November 8, 2019.
Fitaccen Attajirin nan na duniya, Bill Gates wanda shi ne shugaban gidauniyar Bill da Melinda, ya ce harajin da ake karba a Nijeriya ya yi kadan.
Bill Gates ya yi bayanin hakan ne a taron tattaunawa na matasa kan samar da abinci mai gina jiki a Abuja a jiya Talata.
Majiyar mu ta Daily Nigerian Hausa daga Daily Trust ta rawaito cewa, Attajirin dan kasar Amurka yazo Nijeriya ne domin halartar taruka.
Da yake jawabi a taron, Bill Gates, ya ce karancin haraji da ake karba yana haifar da kalubalen kudi a fannin lafiya da ilimi.
Ya ce domin yan kasa su samu karfin gwiwa kan kokarin gwamnati na kula da lafiya dole ne a tabbata ana tafiyar da kudaden da ake warewa fannin lafiya a y...
Najeriya ta zama kasa ta 3 a Duniya wajan yawan cin bashi daga bankin Duniya a karkashin mulkin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.
A shekarar 2024 kadai, Gwamnatin Najeriya ta ciwo bashin jimullar Dala biliyan 2.2 daga bankin na Duniya.
A baya dai kamin zuwan gwamnatin Tinubu, Najeriyarce kasa ta 4 a cikin jerin kasashen da suka fi cin bashin bankin Duniyar.
Kasar Bangladesh ce dai ta daya a Duniya wajan yawan cin bashin daga bankin Duniya, Sai kuma kasar Pakistan ta 2.
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, a kawo musu rahoton duk wani da baya da aikin yi amma yana wadaka da kudade a cikin al'umma.
Ministan ya bayyana hakane a gidan gwamnatin jihar Sokoto.
Yace irin wadannan mutane ka iya zama wakilan 'yan Bindiga masu basu bayanan sirri akan jama'a suna zuwa suna cutar dasu.
Ya kuma nemi jama'ar jihar da su taimakawa jami'an tsaro da bayanan sirri wanda dasune zasu yi amfani wajan samun nasara.
Ministan ya ziyarci jihar ta Sokoto tare da shuwagabannin hukumomin tsaro ne bisa umarnin shugaban kasa dan magance matsalar tsaro.
Hukumomi a matatar man Dangote sun bayyana cewa idan 'yan kasuwar man fetur din suka ki sayen mansu,zasu fitar da man zuwa kasashen waje su sayar.
Mataimakin shugaban bangaren Oil and Gas na matatar, Devakumar Edwin ya bayyana hakan a shirin Berekete Family.
Yace 'yan kasuwar sun musu haka akan Gas da man jirgin sama suka yi saye a hannunsu suka rika zuwa kasashen waje suna siyowa, yace dole saidai sayar da gas din da man jirgin saman suka rika yi zuwa kasashen waje.
Yace idan 'yan kasuwar suka musu haka akan man fetur da suka fara samarwa shima zasu fitar dashi zuwa kasashen waje su sayar.
Wannan hoton na manyan 'yan siyasar Najeriya ya dauki hankula sosai inda aka ga Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Atiku Abubakar da Peter Obi a cikin mota daya.
Kungiyar kwadago ta NLC ta soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan Karin kudin man fetur din da aka yi inda ta zargeshi da yaudara.
Kungiyar tace Tinubu ya yaudaresu suka amince da Naira dubu 70 a matsayin mafi karancin Albashi bisa alkawarin ba za'a kara farashin man fetur ba amma ya yaudaresu.
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya bayyana hakan a cikin sanarwar inda yace suna kiran a janye wannan kari ko su dauki mataki.
Yace zasu ci gaba da kasancewa tare da mutane a kowane irin hali.
'Yan Bindiga a babban birnin jihar Naija watau Minna sun shiga wani rukunin gidaje me suna M.I Wushishi Estate inda suka lalata ababen hawa sannan suka yi gargadin a tashi daga gidan ko kuma idan suka dawo zasu kashe duk wanda suka iske.
Wani shaidan gani da ido yace lamarin ya farune da rana tsaka.
Yace maharan sun shiga rukunin gidajenne yayin da mazajen gidan ke wuraren aiki.
Kakakin 'Yansandan jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace amma yanzu kura ta lafa.
Evoto
Tauraruwar Fina-finan Hausa,Rahama Sadau ta sakarwa masoyanta sabbin hotuna a shafin ta na sada zumunta inda da yawa suka yaba.
Evoto
Evoto
Evoto