Friday, January 10
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Hoto: ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Karbar Adai-daita Sahu Na Sata

Hoto: ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Karbar Adai-daita Sahu Na Sata

Tsaro
Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu matasa biyu da ake zargi da karbar babur mai uku na sata. Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta samu ranar Alhamis, inda ta ce ta kuma kwato babur din da aka sace. “A ranar 28 ga watan Mayu, 2024, rundunar ‘yan sandan Adamawa ta samu bayanai game da wani keken napep da aka sace a kan titin Chochi, Rumde, Yola ta Arewa” in ji rundunar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai daukar hotonta na SP Suleiman Nguroje. “Bayan samun labarin, an tura tawagar ‘yan sanda masu sanya ido a hedikwatar Jimeta Divisional ba tare da bata lokaci ba. An yi sa’a, an kama wani Yusuf Adamu mai shekara 18 da kuma Abdul Salam Abubakar mai shekaru 18 a lokacin da suke kokarin sayar da babur din,” in ji ‘yan sandan. ...
YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

Siyasa
YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe. Majiyar mu ta a yau ta ruwaito Shugaban ya ce yana bakin ƙoƙarinsa a matakin tarayya amma ya kamata a sanya ido kan Gwamnoni su ma su riƙa yin abunda ya dace, su taimaki talakawa, "A lokacin zaɓe ana bin mutane lungu-lungu, gida-gida don neman ƙuri'unsu amma da zaran anci zabe sai kaga Gwamna ko dan siyasa ya tare a Abuja ya mance da talakawansa" inji Tinubu. Me zaku ce?
Na fice daga Kannywood har karshen duniya kuma naji dadin hakan>>Abdul Sahir

Na fice daga Kannywood har karshen duniya kuma naji dadin hakan>>Abdul Sahir

Kannywood
Jarumi kuma mawaki Abdul sahir wanda akafi sani da Mallam Ali na kwana casa’in ya ce ya fita daga masana’antar kannywood daga yau alhamis 30-05-2024, yace yayi hakan ne don samar wa kansa nutsuwa. Idan zaku iya tunawa hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar kano karkashin jagorancin Abba elmustapha ta dakatar dashi daga shiga fina-finan hausa tsawon shekaru 2, sakamakon wani vidiyon da jarumin ya saka, wanda hukumar ke ganin ya sabawa doka da tarbiyyar jihar kano. Mallam Ali na kwana casa’in ya fice daga kannywood, shin ko waye zai maye gurbinsa acikin kwana casa’in?
Kalli Bidiyon yanda aka hada irin dakin Ka’aba a Najeriya dan koyawa Alhazai yanda zasu yi aikin Hajji, saidai wasu sun ce hakan Bidi’a ne saboda Annabi(SAW) bai ce a yi ba

Kalli Bidiyon yanda aka hada irin dakin Ka’aba a Najeriya dan koyawa Alhazai yanda zasu yi aikin Hajji, saidai wasu sun ce hakan Bidi’a ne saboda Annabi(SAW) bai ce a yi ba

Hajjin Bana
Bidiyon yanda aka hada irin dakin Ka'aba a Najeriya ake koyawa mahajjata yanda zasu yi aikin Hajji ya watsu a shafukan sada zumunta. Mutane da yawa sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. https://twitter.com/LifeSaudiArabia/status/1795470560224583895?t=CHtszFt-1PKa3DNX791TJw&s=19 Akwai wanda suke ganin cewa babu abinda Ma'aiki, Annabi Muhammad(SAW) ya bari be koyar da al'umma ba dan haka yin wannan abu tunda annabi(SAW) bai yi ba kuma bai ce ayi ba bai kamata ba. A bidiyon dai an ga wani daki me kama da na ka'aba, mutane sanye da fafaren kaya suna zagayashi, kamar dai a Makkah. Saidai inda mutum zai gane ba dakin ka'aba bane, ga mutane na gefe suna kallo, sannan kuma ga gurin kasa ne, ba kamar a saudiyya ba.

Adduar yaye damuwa

Addu'a
Kana fama da yawan damuwa? Akwai addu'o'i wanda zaka iya yi wanda da yardar Allah zaka samu waraka. Na farko dai idan kana da lokaci, babban maganin damuwa shine karatun Al-Qurani, Musamman idan kasan fassarar abinda kake karantawa. Abu na biyu idan kai me yawan aiki ne ko baka cika samu ka zauna ba sosai. Akwai addu'a da zaka iya yi kamar haka: "La'ilaha illallahul Azimul hakim, la'ilahaillallahul hakimul karim, la'ilaha illallah, subhanallah, rabbussamawatis saba'i wa rabbul arshil azim, Alhamdulillahi Rabbil Alamin" Kai ta maimaitawa iya iyawarka, insha Allahu za'a samu warakar damuwa.