Shugaban kasaz Bola Ahmad Tinubu da 'yan majalisa kenan a wannan bidiyon suke rera sabon taken Najeriya.
Tinubu ya sakawa sabuwar dokar data samar da taken Najeriyar hannu.
https://www.youtube.com/watch?v=KrBJr-gaMro
Wannan matar ta rika bi titi tana lika hotunan wata budurwa data ce ta mata kwacen miji.
Bidiyon lamarin ya dauki hankula kuma ya watsu a shafukan sada zumunta:
https://www.youtube.com/watch?v=_aSX_McPpos
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar canza taken Najeriya.
Wannan yana nufin daga yanzu za a daina National Anthem na "Arise O Compatriots" za a koma yin tsohon National Anthem da aka yi zamanin turawa "Nigeria, We hail thee".
Shin kuna marana da wannan mataki da shugaba Tinubu ya dauka ?
Tauraruwar BBNaija, Alexandra Asogwa wadda aka fi sani da Alex Unusual ta bayyana cewa, har yanzu bata rasa budurcinta ba.
Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta.
Abin ya baiwa mutane mamaki ganin cewa shekarunta 28 kuma musamman a wannan zamanin da ake ciki.
A baya an yi zargin cewa tana lalata da me wasan barkwanci, AY, amma ta fito ta karyata wannan zargi.
YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan:
Wanda ya rubuta - Lilian Jean Williams (1960) wanda yayi kidansa - Franca Benda
Ga Sabon Taken National Anthem din Nigeria ⤵️
Nigeria, we hail thee,Our own dear native land,Though tribe and tongue may differ,In brotherhood, we stand,Nigerians all, and proud to serveOur sovereign Motherland.
Our flag shall be a symbolThat truth and justice reign,In peace or battle honour’d,And this we count as gain,To hand on to our childrenA banner without stain.
O God of all creation,Grant this our one request,Help us to build a nationWhere no man is oppressed,And so with peace and plentyNigeria may be blessed.
Ku bayyana mana ra'ayinku kan wannan mataki da shugaban kasa ya dauka na canja taken Najeriya....
Babban Alkalin Najeriya, Olukayode Ariwoola ya kira Alkalin babbar kotun tarayya dake Kano da alkalin babbar kotun jihar Kano kan Shari'ar masarautar Kano.
Babbar kotun tarayya dake da zama a Kano ta bayar da umarnin sauke Muhammad Sanusi II daga kan kujerar sarautar Kano inda tace a mayar da sarki Aminu Ado Bayero.
Saidai ita kuma babbar kotun Kano ta tabbatar da Sarki Muhammad Sanusi II a matsayin sarkin Kano inda tace a fitar da Sarki Aminu Ado Bayero daga Masarautar Nasarawa da yake zaune.
Wannan lamari ya kawo rudani sosai inda aka rasa wane hukunci za'a yiwa biyayya.
Babban alkalin na kasa ya kirasu alkalan Kanon ne inda yace zasu zauna dan tantance hurumin kowace kotu da kuma tabbatar da aka yin hukunci na bai daya.
Sannan kuma Sanarwar tace za'a yi kokarin ganin iri...
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Hafiz Abubakar ya kaiwa me martaba Sarki Muhammad Sanusi II ziyarar Mubaya'a.
Wadannan hotunane daga ziyarar da ya kaiwa sarkin:
A ranar Laraba, Gwamnatin tarayya ta janye zarge-zarge 3 na ta'ddanci da takewa shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo.
Tun a watan Janairu ne dai sojoji ke tsare da Bodejo bisa wannan zargi inda suka ki bayar da belinsa.
Saidai a ranar Laraba da Ministan Shari'a ya je gabatar da Zarge-Zargen da akewa Bodejo dan ci gaba da shari'a, sai ya ce gwamnati ta janye karar data shigar akanshi.
Wannan lamari dai ya zowa mutane da mamaki ganin cewa a baya gwamnatin ko beli ta ki yadda ta bayar da Bodejon.
Ana dai zargin Bidejo ne da kafa wata kungiyar Funali wadda ake zargin ta ta'ddanci ce da kuma basu makamai da sauran kayan aiki.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a shekarar 2023 ya bayyana cewa, ya shirya mulkin Najeriya amma Shugaban kasaz Bola Ahmad Tinubu bai shirya ba.
Saidai Atiku yace amma Tinubu bai makara ba, zai iya daukar matakan da suka kamata wajan magance matsalolin kasarnan idan da gaske yake.
Atiku ya bayyana hakane a sakon da ya fitar na cikar mulkin Bola Ahmad Tinubu shekara daya akan mulki.
Ya kara da cewa, Tinubu da mukarrabansa basu san hanyar da zasu dauka ba wajan magance matsalolin Najeriya, suna canki cankane akan abinda suke tunanin zai iya yin aiki.
Hukumar Kula da gididdiga ta kasa NBS ta bayyana cewa kudin da mutum zai kashe ya ci abinci me gina jiki a Najeriya ya kai Naira 1,050 a kullun.
NBS ta bayyana hakane a wani rahoto data fitar ranar Laraba akan farashin abinci me gina jiki.
Tace a watan Maris, Naira 982 ake kashewa wajan cin abinci me gina jiki yayin da a watan Afrilu ya karu zuwa Naira 1,050.
NBS tace wannan farashin abincine da bashi da tsada wanda kuma ake samunsa a gida Najeriya amma kuma yana da duk sinadaran da Duniya ta yadda dasu na gina jiki.
Yayin da hukumar ta fitar da kudin da ake kashewa wajan cin abinci me gina jiki a kowane bangare na Najeriya, tace bangaren Arewa maso yamma nan ne ake kashe kudi mafiya karanci wanda suka kai Naira 781 wajan cin abinci me gina jiki a kullun.
Jihohin Kudu maso y...