Rage kiba cikin gaggawa
Ana iya rage kiba cikin sauri ta hanyar amfani da wadannan hanyoyi:
Yin Azumi
Yin Azumi na daya daga cikin manyan hanyoyin rage kiba sosai, ko kun tuna yanda mutane ke ramewa da azumin watan Ramadana?
To idan mutum na son ramewa ko rage kiba cikin gaggawa, to yayi azumi,ana iya yin Azumin Litinin da Alhamis dan samun sakamako me kyau.
Daina shan Zaki
Idan ana son rage Kiba cikin gaggawa a daina ko a rage shan zaki, watau zaki irinsu lemun kwalba, Yegot/Yoghurt da sauransu.
Ana iya rika amfani da zuma, Mazarkwaila, rake da sauran hanyoyin samun zagi wanda ba na bature ba ko suma ayi amfani dasu saisa-saisa.
A rage Amfani da kayan da bature ya sarrafa:
A rage cin kayan da aka sarrafa na roba, leda, da kwalba, a yawaita amfani da kayan da aka hada a gida maimakon na ka...