Sunday, January 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba’a gano inda take ba

Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba’a gano inda take ba

Katsina, Rarara, Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, awanni 24 bayan yin garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, Rarara har yanzu, ba'a gano inda take ba. Kakakin 'yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa an kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da mahaifiyar Rarara din amma har yanzu ba'a gano inda take ba. Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan Bindigar da suka je yin garkuwa da mahaifiyar Rarara sun je ne a kafa tike da muggan makamai suka shiga gidanta suka kamata. Rahoton yace Bata musu gaddama ba kuma babu wanda ya tunkaresu saboda muggan makaman da suke dauke dasu. Daily Trust tace ta nemi jin ta bakin Rarara amma bata yi nasara ba saboda wayoyinsa duk a kulle kuma an aika masa da sakon waya amma bar bayar da amsa ba.
Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban da ba'a taba yin irinsa ba wajan jajircewa da yiwa Najeriya aiki. Ya bayyana hakane jiya kamar yanda jaridar thisday ta bayyana. Yace shugabanci ba da karfin jiki ake yinsa ba, da kaifin tunani ake yinsa dan haka a daina alakanta lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin da yake. Ya kuma yi Allah wadai da wadanda suka rika yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dariya a ranar Dimokradiyya data gabata.
Duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’>>Inji Amal Umar

Duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’>>Inji Amal Umar

Amal Umar
Jarumar fina-finan Kannywood, Amal Umar ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu mutane na yaɗa mummunar fahimtarsu game da halayen wasu jaruman shirya fina-finan. Amal Umar -wadda ta bayyana hakan cikin shirin Mahangar Zamani na BBCHausa - ta ce babban takaicinta shi ne yadda ake yi wa ƴan fim kallon marasa tarbiyya. Duk da cewa akwai labarai marasa daɗi da ake yaɗawa game da masu sana’ar fim, jarumar ta nesanta kanta daga dukkan zarge-zargen da al'umma ke yi wa 'yan fim. ‘’Kowa ba ya yi mana zaton alkahiri, sai dai ki ji ana karuwai ne su, ba su kwana a gidajensu, sun raina iyayensu, irin waɗannan abubuwan, amma ni na sani, kuma masu mu’amula da ni sun sani, duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’, in ji jarumar. Sauran baƙin da shir...
Bidiyo ya bayyana na ma’aikaciyar gwamnati, matar aure me yara 2 ana làlàtà da ita a wajan aikinta

Bidiyo ya bayyana na ma’aikaciyar gwamnati, matar aure me yara 2 ana làlàtà da ita a wajan aikinta

Abin Mamaki
Wata mata ta dauki hankula a shafukan sada zumunta a yau, Asabar bayan da bidiyo ya bayyana ana lalata da ita a wajan aikinta. Matar dai ma'aikaciyar gidan yari ce a kasar Ingila. Matar an ganta a wani bidiyo da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta daya daga cikin masu laifi da ake tsare dasu yana lalata da ita turmi da tabarya. Wani abin karin mamaki shine ita dai wannan mata tana da miji hadda yara 2. Matar dai 'yar asalin kasar Brazil ce kuma tuni aka kamata aka fara bincike akanta

Menene sunan awara da turanci

Sunaye
Sunan Awara da turanshi shine Soybean cake. Awara na daya daga cikin abunci masu arha da ake amfani dasu wajan kawar da yunwa cikin gaggawa a arewacin Najeriya. Hakanan ana cin awara dan marmari. Kasancewar ana amfani da waken suya ne wajan yinta, yana taimakawa sosai wajan gina jiki.

Menene sunan alkama da turanci

Sunaye
Sunan Alkama da turanci shine wheat. Ana sarrafa Alkama ta hanyoyi daban-daban a al-adu daban-daban na Duniya. Misali a Arewacin Najeriya, ana sarrafa alkama a yo tuwon furfushe, Burabusko, Fankaso, Fulawa da sauransu. Alkama na daya daga cikin abubuwan daka fi ci a fadin Duniya baki daya.

Kalolin ruwan gaban mace

Gaban mace
Kin taba tunanin ko kalolin ruwan dake fita daga gaban mace guda nawane? A wannan rubutun,mun kawo muku cikakken bayani kan yawan kalolin ruwan dake fita daga gaban mace da kuma ma'anar kowanne. Ga su kamar haka: Ruwan dake fita a gaban mace abune da yawancin mata sun saba dashi, kuma yana fitane dan wanke da tsaftace gaban macen daga lokaci zuwa lokaci. Ba abune na tashin hankali ba amma ya kamata a lura da canje-canje a kalolin ruwan da kuma yanayin jiki wanda ka iya sanyawa a gane shigar cuta. Fitar Farin Ruwa: Farin ruwa wanda wani lokacin yakan iya zama me yauki ko me ruwa-ruwa a gaban mace bashi da matsala. Wani lokacin ma zaki ga ya bata miki wando, a wani lokacin ida kina jin sha'awa zaki iya jin wannan ruwa wanda yana zuwane dan saukaka yin jima'i. Hakanan kum...