Illar yawan fitar da maniyyi
Yawan fitar da maniyyi yana iya haifar da wasu illoli, musamman idan yana kasancewa a kai a kai ba tare da tsari ko natsuwa ba.
Ga wasu daga cikin illolin da za su iya tasowa:
Rauni ko kumburi: Yawan fitar da maniyyi na iya haifar da rauni ko kumburi a al'aurar namiji, musamman idan ana yi ba tare da isasshen lubricator(watau man dake taimakawa wajan jin dadin jima'i ba) ko babu tsari ba.
Gajiya da raunin jiki: Yawan fitar da maniyyi na iya sa mutum jin gajiya da rauni saboda yana bukatar kuzari da karfi sosai.
Tasirin kwakwalwa: Wasu mutane na iya jin gajiya ko damuwa bayan yawan fitar da maniyyi saboda sauyin yanayin hormone da ke faruwa a jiki.
Rage kaifin hankali: Idan yawan fitar da maniyyi ya zama wani nau'i na jaraba, zai iya ragewa mutum da kaifin hankali da rage k...