Tuesday, January 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ko da matatar Dangote ta fara tace man fetur ba lallai farashinsa ya sauko ba>>Inji Masana

Ko da matatar Dangote ta fara tace man fetur ba lallai farashinsa ya sauko ba>>Inji Masana

Kasuwanci
Masana masu sharhi akan al'amuran yau da kullun sun bayyana cewa, ko da matatar man Dangote ta fara aiki ba lallai tasa farashin man fetur ya sauka ba. Masanan aun bayyana dalilan cewa,har yanzu matatar ta Dangote daga kasashen waje take samo danyen man da tame tacewa. Sannan farashin dala dake ta kara hauhawa shima ba lallai ya bayar da damar samun saukin man fetur din ba ko da mamatar ta Dangote ta fara aiki ba. A kwanannan dai Dangote ya bayyana cewa zai ci gaba da shigo da danyen man fetur daga kasar Amurka saboda rashin isashshen danyen man fetur din a Najeriya.
Bamu da Banbanci da shuwagabannin mu: Kalli yanda mutane ke sace naman shanu bayan da motar dake dauke da su ta samu matsala a Kano

Bamu da Banbanci da shuwagabannin mu: Kalli yanda mutane ke sace naman shanu bayan da motar dake dauke da su ta samu matsala a Kano

Kano
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani lamari da ya faru a Kano ya baiwa mutane mamaki inda aka ga mutane na satar naman shanu daga wata mota daga samu matsala. An ga mutane na rige-rigen gudu wasu dauke da kawunan shanu biyu wasu daya. https://www.youtube.com/watch?v=NkZ3yz1QqQY&pp=ygUJZGF0b2RhdHVr Wannan na zuwane a yayin da ake zargin shuwagabannin a matsayin wanda ke satar dukiyar mutane suna biyewa daga su sai iyalansu.
An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

labaran tinubu ayau, Siyasa
An Gudanar Da Addu'ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa …wanda shugaban hukumar kula da almajirai ta kasa ya jagoranta a yau Juma'a Daga Mustapha Narasulu Nguru Shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta na kasa, Dr. Muh'd Sani Idriss Phd ya jagoranci addu'a ga mahaifiyar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu GCFR, wanda aka gabatar yau Juma'a. Shugaban hukumar ya yi addu'a a gare ta sosai a yau Juma'a 21/06/2024 a yayin da take cika shekaru sha daya da barin duniya. Cikin jawabansa ya rokar mata rahama ga Allah (SWT) kamar yadda addini ya tanadar. Muna fatan Allah Ya yi mata rahama da sauran y'an uwa musumal. Allah Ya sa Aljannah makoma.
Ji tsokanar da dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi yawa Tsohon Gwamnan Kano, Ganduje

Ji tsokanar da dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi yawa Tsohon Gwamnan Kano, Ganduje

Kano, Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Bayan hukuncin kotu kan rushe sabbin masarautun Kano, lamarin ya jawo cece-kuce a jihar inda mahawara ta yi zafi kuma kowane bangare tsakanin gwamnatin Kano, da Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero ke ikirarin yin nasara, Gwamnatin jihar ta sa a rushe gidan sarki na Nasarawa wanda sarki Aminu ke ciki. A wasu hotuna da bidiyo da suka watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga yanda motocin rushe gida suka je fadar ta Nasarawa. Yayin da yake mayar da martani akan wannan lamari, dan gidan Sarki Muhamma...

Gyaran fuska da tumatir

Gyaran Fuska, Kwalliya
Bayan Amfani a Miya, Tumatir na da wani amfani musamman a wajan gyaran fata da fuska: Ga amfanin da yakewa fuska kamar haka: Tumatur na daidaita man fuska. Idan ya kasance fuskarki me yawan samar da maski ne ko mai wanda bata barin kwalliya ta dade a jikin fuskar, kina iya amfani da tumatur wajan maganin wannan matsala. Yanda ake yi shine: Zaki dauki tumatur ki yankashi gida biyu. Sai ki shafashi akan fuskarki. Ki barshi yayi mintuna 10 akai sannan ki wanke da ruwa. Yin hakan akai-akai zai yi miki maganin yawan maikon fuska. Za'a iya yin Amfani da Tumatur dan kawar da dattin da ya makale a fuska wanda wanki da sabulu baya masa. Akwai abubuwa da yawa irin su dattin masana'antu da sauransu wanda idan suka hau kan fata ko fuska, dan wanka ko wankewa da ruwa baya ...

Gyaran fuska da manja

Gyaran Fuska, Kwalliya
Akwai hanyoyi da yawa da ake gyaran fuska da man ja. Ga wasu daga ciki kamar haka: A wanke fuska dan fitar da duk wani datti, a saka tsumma a tsane fuskar. Daga nan sai a shafa man ja, a bari ya dan jiku a fuskar sai a goge. Hakan yana kawar da duk wani duhun fata. Ana kuma iya diga man ja a cikin man shafawa ko man wanka da sauransu. A wani kaulin, an ruwaito man ja na kawar da tabon kuna wanda bai yi zurfi ba sosai, sannan yana kawar da tabon kurajen fuska da yankewa wadda bata yi zurfi ba sosai. Hakanan wani kaulin ya bayyana manja na maganin tattarewar fuska ta tsufa, fuskar mutum ba zata tattare sosai ba.
Shugaba Tinubu ya saka jiragensa 3 a kasuwa

Shugaba Tinubu ya saka jiragensa 3 a kasuwa

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta sanar da saka jiragen shugaban kasar guda 3 a kasuwa dan sayarwa. Jiragen dai sun tsufane shine aka tattara za'a sayar dan samun kudaden da za'a siyo sabbi. Wannan mataki kuma zai rage kudaden da ake kashewa wajan kula da jiragen wanda ba duka Shugaban kasar ke amfani dasu ba. Hakan na zuwane yayin da majalisar tarayya ta bada shawarar saiwa shugaban kasar da mataimakinsa sabbin jirage.
Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

Duk Labarai
'Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da satar mota kirar Toyota Corolla. Kakakin 'yansandan na Abuja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da lamarin inda yace an kamasu ne ranar Juma'a. Yace an kamasu ne a yayin da suke kokarin sayar da Motar a kan Naira Miliyan 6.5 a Minna. Wadanda aka kama din sune, Gwaza Bulus san kimanin shekaru 41 da kuma Yahya Amodu dan kimanin shekaru 45. Ana ci gaba da bincike kan lamarin.