Ba mu ƙara kuɗin da muke kashewa a tallafin man fetur ba – NNPCL
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya musanta rahotannin da ke cewa ya kara kudin tallafin man fetur da sama da naira tiriliyan uku a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye, ya jaddada cewa an tabbatar da ikirarin tallafin da kamfanin ya bayar, tare da mika dukkan bayanan da suka dace ga hukumomin da suka dace.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin na NNPCL bai san wani shiri na tantance asusun ajiyarsa ba, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai na farko suka nuna.
"NNPCL ta lura da wani rahoto a wani sashe na kafafen yada labarai da ke zargin cewa ta kara kudin tallafin da naira triliyan 3.3," in ji Soneye.
“NNPCL tana gudanar da kasuwancinta ne cikin gaskiya bisa kya...






