Thursday, January 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gyaran gashi da wiwi

Gyaran Gashi
Tabbas masana sun bayyajan cewa Wiwi na taimakawa wajan gyaran gashi. Saidai Yin amfani da ita ta yanda bai kamata kuma yana sawa gashi ya zube. Saidai amfani da wiwi a wajan gyaran gashi ba wai yana nufin a shata kamar tababa ko a taunata ba. Yana nufin a rika shafata akan gashi dan gashin ya kara girma da tsawo da hana bushewa da karyewa. Masana aun bayar da shawarar cewa ana iya hada man kwakwa ko man zaitun da wiwi a rika shafawa a akai a tabbatar ko ina ya samu. Sannan idan ana son a ga sakamako me kyau, sai an rika shafawa a kullun. Ko kuma idan ba za'a iya shafawa kullun ba, ana iya shafawa sau daya a sati.

Gyaran gashi da kwai

Gyaran Gashi
Ana amfani da kwai, Musamman Gwaiduwar kwai wajan gyaran gashi. Gwaiduwar kwai itace me ruwan dorawa ko Yellow wadda ke cikin kwan idan an cire farin ruwan kwan. Tana da sinadarai masu yawa dake taimakawa armashin gashi irin su biotin, folate, vitamin A, da vitamin D. Mutane na amfani da Gwaiduwar kwai a gashi dan hana gashin zubewa, da kara masa tsawo, da hanashi bushewa da kakkaryewa. Gwaiduwar kwai na hana gashi lalacewa,yana kare gashi daga abubuwan dake sawa ya lalace. Hakanan Gwaiduwar kwai tana saka gashin kai ya rika saurin tofuwa. YANDA AKE AMFANI DA GWAIDUWAR KWAI: Ana iya amfani da Gwaiduwar kwai da man zaitun a kwaba a shafa a kai ko ina da ina ya shiga cikin gashi da kyau. Sannan kuma ana iya amfani da kwan gaba dayanshi ba tare da hadawa da man zaitun ...

Gyaran gashi da ganyen magarya

Gyaran Gashi
Domin yin gyaran gashi da ganyen Magarya,ga bayani a kasa kamar haka: A samo ganyen danyen lalle ko na magarya. A Samo Garin Hulba ko tsaba. A sako man zaitun A samo Man Ridi. A Samo Man Habbatussauda. A samo Man Kwakwa. YADDA AKE HADAWA Ana hada ganyen lalle, Ko na magarya, da garin Hulba a waje daya a zuba a tukunya a tafasa a sauke ya huce, kada a bari ya huce gaba daya,yayi dumi yanda za'a iya wanke kai dashi. Kanki kuma,zaki hada wadancan mayukan da muka ce a samu a sama sai ku shafa sosai akan ya shiga ko ina. Sai ki sa a gashinki a Leda ki daure zuwa mintuna 15. Bayan nan sai ki yi amfani da ruwan hulba da ganyen lalle ko na magarya dincan da kika dafa ki wanke kan. Ki barshi ya bushe. Sannan zaki sake shafa masa mai. Sai ki je a miki kitso. ...

Amfanin karkashi a gashi: Yadda ake wanke kai da karkashi

Gyaran Gashi
Ga yanda ake amfani da Karkashi dan gyaran gashi. Akwai hanyoyi da yawa, ga kadan daga cikinsu: Da farko zaki samu busasshen karkashi ki dakeshi aturmin qarfe sai kisa ruwa mai zafi a bap Na wanka sai ki zuba karkashin Dan dadai sai ki zuba shampoo sai ki saka ruwan toka ko kanwa sai ki kada zakiga yayi kumpa sosai kuma yayi kore shar sai ki tsaga tsakiyan Kai ki raba gashi biyu sai kisa ta sunkuyo cikin bap din sai ki qulle gefe daya ki wanke dayan ruwa ya shiga sosai ki Mirza da kyau sai ki matseshi ki dauko cokali idan kika matse sai ki katse shi da cokali ruwan yana bin jikin cokali har sai kinga ya daina sai ki daure shi sai kiyima dayan gefen ma haka. Idan ya bushe kika taje kan zakiga idan da akwai abin karkashin zai fita sai ki samu mai oil ko zai tun ki shafa shknn Note...

Gyaran gashi da ruwan shinkafa

Gyaran Gashi
Mutanen kasar China da Japan sun dade suna amfani da ruwan shinkafa wajan kara tsawon gashi da kuma hanashi yin furfura. Hakanan kuma a wani kaulin,ruwan Shinkafa na hana gashin mumurdewa da hadewa da juna. Hakanan kuma ruwan shinkafa na karawa gashin kai sheki. Matan wani kauye a China me suna, Huangluo na daga matan da suka fi kowane mata tsawon gashi a Duniya inda aka ruwaito cewa gashin kansu hana kai tsawon kafa 6. Sannan kuma gashin kansu yawanci bai fara yin furfura sai sun kai kusa da shekaru 80 a Duniya. Wadannan mata sun bayyana cewa sirrinsu shine wanke gashin kansu da suke yi da ruwan shinkafa. YANDA ZA'A SAMU RUWAN SHINKAFA DAN GYARAN GASHI Akwai hanyoyi 3 da ake samun ruwan shinkafa dan gyara gashi dashi. Danyar Shinkafa: Ana samun danyar Shinkafa rab...
Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana’antar Kannywood, A’isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri

Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana’antar Kannywood, A’isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri

Kannywood
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRAJI'UN Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana'antar Kannywood, A'isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri. Humaira ta bayyana rasuwar a shafinta na Instagram inda ta nemi al'ummar musulmi da su sanya ta cikin addu'a Allah Ya gafarta mata tare da sauran al'ummar Annabi (S.A.W) da suka riga mu gidan gaskiya. Za a yi mata sallar Jana'iza a gobe da safe, a birnin Maiduguri na Jihar Borno.

Hadin tsawon gashi

Gyaran Gashi
Hadin tsawon gashi Akwai hanyoyi da dama da mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo. Abu ne mai sauki. Mata da dama suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau don haka, ya kamata mu kula da gashinmu sosai. Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi maiko , wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi. Ina son a san cewa wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, ba ya kamata ana hada wannan salon gyaran gashi da wani daban in ba haka ba, sai a ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Abubuwan da za a bukata Man AmlaZumaRuwan dumiHadi A zuba cokalin amla biyu a roba.Sannan sai a zuba rabin cokalin ...

Tsawon gashi cikin sati daya

Gyaran Gashi
Ana iya samun tsawon gashi cikin sati daya idan aka yi abinda ya dace kamar yanda zamu yi bayani a kasa: Hanya ta farko da ake iya kara gashi cikin sati daya itace ta amfani da man kwakwa, ko man Zaitun. Yanda ake yi shine, ana samun man kwakwa ko kan zaitun a dafashi, a sauke ya huce,amma kada a bari ya huce gaba daya, sai a taba da hannu a ji idan akwai dumi yayi daidai yanza za'a iya shafawa akai sai a rika dangwala ana shafawa akai, a shafa sosai ya shiga cikin gashi da kyau. A tabbatar an gauraye duka gashin dashi. A bari yayi mintuna akalla 30 sannan a wanke da shampoo. Hakanan masana sun kara da cewa, cin abinci me gina jiki da kyau da kuma motsa jiki da kuma murza gashin kai akai-akai watau a rika yi mai tausa har zuwa inda ya tsiro yana taimakawa kara yawan gashi sos...