Tuesday, February 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu kan zargin garkuwa da mutane a dazukan Abuja

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu kan zargin garkuwa da mutane a dazukan Abuja

Tsaro
Rundunar 'yan sandan birnin Abuja, tare da haɗin gwiwa dakarun sahen yaƙi da manyan laifuka da 'yan sanda farin kaya, da mafarauta, sun wargaza sansanonin wasu 'yan bindiga a ƙauyen Gidan Dogo da dajin Kweti da ke kan iyakar Abuja da Kaduna. Cikin wata sanarwar jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan birnin, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce bayan samun bayanan sirri, jami'an tsaron suka kai samame dajin ranar 7 ga watan Mayu, in da suka kama mutum huɗu da suke zargi. Sanarwar ta ce mutanen da suka kama, sun faɗa wa 'yan sanda cewa suna cikin wani gungun masu garkuwa da mutane mai suna, 'Mai One Million', waɗanda suke da alhakin kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a birnin Abuja da kewaye. 'Samamen wanda aka samu musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, ya tilasta wa 'ya...
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga biyar tare ƙwato makamai a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga biyar tare ƙwato makamai a Kaduna

Tsaro
Sojojin Najeriya da ke aiki da rundunar 'Operation Whirl Punch' mai yaƙi da masu garkuwa da mutane sun kashe 'yan bindiga biyar a yankin Dantarau da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna. Cikin wata sanarwa da kwamishin tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce dakarun sojin waɗanda ke aiki a yankunan ƙananan hukumomin Kachia da Kajuru sun kuma ƙwato makamai. ''Sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, ƙwason zuba alburushi na Ak-47 guda tara, da harsasai 250 da babura biyu da wayoyin oba-oba biyu'', in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun kuma lalata sansanonin 'yan bindigar a yankin Sabon Birnin Daji da ke ƙaramar hukumar Igabi. Aruwan ya kuma ce a lokacin samamen sojojin sun yi musayar wuta d...

Maganin aljani mai taurin kai

Addu'a
Ga maganin Aljani kamar yanda yazo a Sunnar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam). Na daya shine a nemi tsarin Allah daga shaidan, Watau fadar A’udhu Billahi min al-Shaytan il-rajim. Sulayman ibn Sard ya ruwaito cewa, wasu mutane na ta zage-zage a gaban Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) har fuskar daya daga cikinsu ta yi ja. Sai Annabi Muhammad(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace da mutumin zai fadi wasu kalmomi da abinda yake ji ya gushe, watau fadar ‘A’udhu Billahi min al-Shaytan il-rajim.  (al-Bukhari and Muslim). Karanta Falaki da Nasi. Abu Sa’id al-Khudri Allah ya kara yadda dashi ya ruwaito cewa, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana neman tsari daga sharrin mutum da aljani, amma bayan da aka saukar da Falaki da Nasi, sai ya k...
Gwamna Buni Ya Yi Watsi Da ‘Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi

Gwamna Buni Ya Yi Watsi Da ‘Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi

labaran jihar yobe state, Siyasa
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi watsi da matakin bai wa kananan hukumomin kasar ‘yancin cin gashin kansu. Buni ya bayyana ra’ayinsa ne jim kadan bayan kada kuri’arsa a zaben kananan hukumomi a mazabar sa da ke Buni Gari. “Lokacin da na hau mulki a shekarar 2019, tunanina shi ne in ba kananan hukumomi cin gashin kai. Sai dai abin takaici shi ne kananan hukumomi shida cikin 17 na jihar Yobe ba sa iya biyan ma’aikata albashi. “Saboda haka, hikimar da ke tattare da wannan asusun hadin gwiwa, wanda ya hada da kokarin kananan hukumomi tare da jihar tare da hadin gwiwa wajen aiwatar da wasu ayyuka, ra’ayi ne da aka samu daga wadannan gazawar,” in ji shi. Gwamnan ya kuma bayyana fatansa game da makomar cin gashin kan kananan hukumomi a Najeriya. "Dimokradiyyarmu tana girma,...
Jihohi 22 sun kashe Naira Biliyan 251 wajan Biyan Bashi a cikin watanni 9

Jihohi 22 sun kashe Naira Biliyan 251 wajan Biyan Bashi a cikin watanni 9

Siyasa
Jihohi 22 a Najeriya sun kashe Naira Biliyan 251.79 wajan biyan bashin da gwamnatocin da suka gada suka bar musu cikin watanni 9 da suka yi suna mulki. Hakanam kuma jihohin sun ciwo bashin Naira biliyan 310.99 a tsakanin wannan lokaci. Sun ciwo wadannan basukanne duk da kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya wanda ake tura musu duk wata. Hakan na kunshene a cikin bayanan yanda kowace jiha ta aiwatar da kasafin kudinta dake runbun tattara bayanai na Open Nigerian States. Jihohin dai sune Abia, Akwa Ibom, Anambra, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Niger, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara. Jihohin dai sun gaji jimullar bashin Naira Tiriliyan 2.1 dana dala Biliyan 1.9. Jihohin dai sun gaji basukan a...
Kalli Hoton Duniyar Mars da aka dauko daga sararin samaniya, Saidai da yawa na cewa basu yadda da hoton ba

Kalli Hoton Duniyar Mars da aka dauko daga sararin samaniya, Saidai da yawa na cewa basu yadda da hoton ba

Abin Mamaki
Wannan hoton, Tauraron dan Adam mallakin hukumar sararin samaniya ta kasar Amurka, NASA ce daukoshi daga Duniyar Mars, Saidai mutane da yawa sun ce basu yadda ba. An dai dauki hoton ne a ranar 6 ga watan Yunin 2024 da muke ciki. https://twitter.com/MarioNawfal/status/1799797996059554084?t=dL0PGQzE548EtTrzSvEUkA&s=19 Hoton dai yayi matukar kama da Duniyar da muke ciki.
Jin dadin Mulkin Tinubu yasa Gwamnatin jihar Sokoto ta sakawa daya daga cikin Titunan jihar sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu

Jin dadin Mulkin Tinubu yasa Gwamnatin jihar Sokoto ta sakawa daya daga cikin Titunan jihar sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu

Siyasa, Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Ali na fuskantar caccaka daga bakunan da yawa daga cikin 'yan Najeriya bayan sakawa wani titi a jihar Sokoto sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu. Kafar Peoplesgazette ta bayyana cewa tsohon sunan titin shine Pepsi Road. Tace kuma a ranar 3 ga watan Yuni ne ya kamata a kaddamar da titin amma hakan bata samu ba.
Kalli Hoton mutumin da ya sa-yar da ‘ya’yan cikinsa har guda 6 a jihar Sokoto

Kalli Hoton mutumin da ya sa-yar da ‘ya’yan cikinsa har guda 6 a jihar Sokoto

Abin Mamaki
An kama wannan mutumin me suna Malam Bala Abubakar a jihar Sokoto bayan samunaa da laifin sayar da yara har guda 28. Wani abin mamaki ma shine cikin yaran da ya sayar hadda 'ya'yansa guda 6. An dai yadda da Malam Bala Abubakar a matsayin me kula da marayu. Hukumar 'yansanda ta jihar Sokoto tace yana sayar da yaranne ga wasu mata Elizabeth Oja da Kulu Dogonyaro da sunan za'a kai yaran Abuja dan wani mutum ya rika basu kulawa me kyau. Malam Bala dai yana zaunene a unguwar Tudun Wada dake jihar Sokoto. Kuma wanda suka sanshi sun yi mamakin abinda ya aikata. Lamarin dai yana hannun 'yansanda inda ake ci gaba da bincike.
DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan Crypto sun sa ankulle Tweeter account din Naziru Sarkin Waka

DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan Crypto sun sa ankulle Tweeter account din Naziru Sarkin Waka

Kannywood, Nazir Ahmad Sarkin Waka
Hakan ya samo asali ne bayan zagin da yayi wa 'yan mining inda yake cewa " Iya mining ɗinka iya talaucin ka" ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da yake yawo a kafofin sada zumunta. Kalaman da mawakin yayi yayi matuƙar da hankulan yan Crypto wanda yakai ga har sun fara fitowa kafofin sada zumunta suna mayar masa da martani, daga bisa ni kuma suka fara turawa mai kampanin tweeter korafin su, wanda daga karshe korafin su ya samu karbuwa har yakai ga an tsaida a shafin sa na tweeter a halin yanzu. Zuwa yanzu sun koma tura korafin su ga sauran kampanonin sada zumunta inda yake da account dasu kama daga facebook, tiktok Instagram. Shin ya kuke ganin matakin da suka ɗauka ?