Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kiwon Lafiya
Wata cuta da aka kira da Ring worms dake yaduwa ta hanyar Jima'i ta bayyana. Cutar dai wadda irintace a karin farko da aka gani a jikin dan adam ta bayyana ne a jikin wani dan kasar Amurka. Mutumin dai dan Luwadi ne wanda kuma yaje kasashe daban-daban yayi lalata da maza masu yawa. Bayan da ya koma kasarsa ta Amurka ne sai aka ganshi da wannan cuta. Saidai masana kimiyyar lafiya sun ce kada mutane su tayar da hankali dan cutar bata kai matakin barazana ga sauran al'umma ba. Ko da dai cutar Kanjamau akwai wasu majiyoyi dake cewa daga wajan 'yan Luwadi aka fara samota, hakanan ta tabbata cewa masu Luwadi sun fi saurin kamuwa da cutar.
Sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zai sauko a Najeriya>>IMF

Sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zai sauko a Najeriya>>IMF

Siyasa
Hukumar bada lamuni ta Duniya, IMF ta bayyana cewa, sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zasu sauko kasa. Tace ta yi hasashen farashin kayan masarufin zai sauko da kaso 15 cikin 100 nan da shekarar ta 2029. A yanzu dai, Alkaluman kayan masarufi a Najeriya sun kai maki 33.69 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana. Tun dai bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ne dai aka shiga tsadar rayuwa wadda har yanzu babu alamar zata kare. Ko da a jiya, saida Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, zata sake daukar matakai masu tsauri wanda ka iya kara jefa 'yan Najeriya cikin halin matsi. Saidai Gwamnatin tace wadannan matakai da take dauka kokarine na tada komadar tattalin arziki.
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira dubu sittin da biyu (62,000) a matsayin sabon tayin mafi karancin Albashi

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira dubu sittin da biyu (62,000) a matsayin sabon tayin mafi karancin Albashi

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira Dubu sittin da biyu a matsayin sabon tayinafi karancin Albashi ga kungiyar Kwadago. Hakanan Sabon rahoton ya bayyana cewa, kungiyar kwadago ta NLC ta sauko daga matsayin ta na cewa gwamnati ta biyata Naira dubu dari hudu da chasa'in da hudu(494,000) inda a yanzu tace a biyata Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000). Tuni dai kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da tayin na gwamnatin tarayya watau dubu 62,000.
DA ƊUMI-ƊUMI: Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba>>Gwamnoni

DA ƊUMI-ƊUMI: Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba>>Gwamnoni

Siyasa
Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun ki amincewa da tayin Naira dubu 60 mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta ga. Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, Hajiya Halimah Salihu Ahmed ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a. A tuna cewa a ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, suka shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan sun ki amincewa da tayin N60,000 da gwamnatin tarayya tayi a matsayin mafi karancin albashi. Amma daga baya sun sanar da cewa za su sassauta yajin aikin na tsawon mako guda domin ba da damar tattaunawa da gwamnatin tarayya, wadda ta yi alkawarin kara albashin daga N60,000. Sai dai gwamnonin sun ce mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 60 ba mai yiwuwa ba n...
Mu daina jin tausayin Mutane, idan Allah ya dandana musu, suka sha wuya zasu dawo hayyacinsu>>Dr. Ahmad Gumi akan yanda mutane suke wulakanta kansu a wajan masu rike da mukamai da kuma kasa kalubalantar Azzaluman shuwagabanni

Mu daina jin tausayin Mutane, idan Allah ya dandana musu, suka sha wuya zasu dawo hayyacinsu>>Dr. Ahmad Gumi akan yanda mutane suke wulakanta kansu a wajan masu rike da mukamai da kuma kasa kalubalantar Azzaluman shuwagabanni

Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa a kyale mutane su dandana wahalar Rayuwa watakila hakan zai sa su shiga taitayinsu ta yanda zasu rika kalubalantar azzaluman shuwagabanni. Ya bayyana hakanne da yammacin yau, Juma'a, 7 ga watan Yuni yayin da yake karatun littafin Muktasar a masallacin Sultan Bello dake Kaduna. Malam ya kara da cewa, mutane suna da wakilai a majalisar tarayya idan akwai abinda basa so zasu iya gayawa wadannan wakilai cewa shugaban kasa ya canja idan ba haka ba ...