Hotuna:’Yan Boko Haram 3 da iyalansu sun mika wuya gurin sojojin Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan Boko Haram 3 da iyalansu sun mika wuya inda sukace sun tuba ga sojojin Najeriya.
'Yan Boko Haram din masu sunan Umar Ibn Khatab, Ibn Salih da Abdulrahman sun mika kansu ne ranar 29 ga watan Mayu.
Sun tsere ne daga maboyarsu dake Njimia bayan da sojoji suka bude musu wuta.
Sun kuma mika bindigun AK47 da harsasai da keke.