Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna ‘Katsina babu ƙorafi’ ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa.

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa yace a matsayinsa na gwamna, bai da masaniya dangane da kafa wani allo da ke nuna cewa Al’ummar Jihar ba su da ƙorafi bisa ga salon Mulkin shugaba Tinubu ba.
Hasalima Gwamnan yace, sun gabatar ma shugaba Tinubu ƙwararan ƙorafe-ƙorafe har guda 3 da ke buƙatar a magance masu, wanda suka haɗa da Matsalar tsaro, kammala wuta mai amfani da hasken Rana, da kuma fadada filin sauka da tashin jirage na Umar Musa Yar’adua da ke Katsina.
Bayan haka ya ja hankalin masu suka da su riƙa tantance labarin da suka gani a kafafen sada zumunta domin tabbatar da asalin labarin, kafin sukar wanda baya da masaniya a kai.
Daga Lukman Aliyu