Tuesday, February 24
Shadow

Ba gudu ba ja da baya sai mun yi zàngà-zàngàr da muka shirya>>Inji Kungiyar Kwadago bayan ganawa da shugaba Tinubu

Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, babu gudu ba ja da baya ta shirya tsaf dan ci gaba da zanga-zangar data shirya ayau.

Hakan na zuwane bayan ganawar da kungiyar ta yi da shugaba Tinubu a daren ranar Talata.

Shuganan NLC, Joe Ajaero ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar NLC cewa zasu fita zanga-zangar da suka shirya yau ba fashi.

Tuni hukumar ‘yansandan Najeriya ta sanar da kai jami’an ta na musamman gurare daban-daban dan hana bata gari shiga zanga-zangar su batata.

Karanta Wannan  Kungiyoyin Arsenal, Man City, West Ham, Leicester, Man United, Bybit, Kasar Amurka, Real Madrid, Jami'ar Oxford da sauransu sun taya Musulmai murnar shiga watan Ramadana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *