
Matar marigayi tsohon shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta bayyana cewa, ba zata sake yin wani aure ba.
Hajiya A’isha ta bayyana hakane a littafin da aka rubuta na rayuwar tsohon mijinta, kuma tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Tace miji daya ya isheta.
Sannan kuma tace zata ci gaba da rayuwa a tsakanin ‘ya’yanta da Jikoki da abokai.
Tace zata ci gaba da kula da gidauniyarta.