Daga Dan Bala
A farkon shekarar 2021 an samu yawaitar jita-jita cewar wai jirage na zuwa su kawowa ƴan bìđìģa màķàmai su kuma ɗauki gwal a asirce (ba wannan ba ne karo na farko da ake samun irin wannan jita-jitar).
Malam Abdulaziz Abdulaziz a matsayin sa na ɗan jarida mai bincike, ya yi tafiya zuwa Zamfara don binciken gani da ido ya kuma kuma tattauna da masana harkokin sauka da tashin jiragen sama (tare da taimakon Mal Hussaini Jibrin).
Binciken ya tabbatar da wannan zancen ƙanzon kurege ne kawai, ya kuma ƙaryata maganar cewa jirgi zai iya shigowa Najeriya ba tare da an gan shi ba.
Na yi sharing wannan labarin ne don na ga ana neman dawo da wannan maganar marar tushe tare da harma ana cewa radar mai ganin jirage sararin samaniya Najeriya ta lalace shekaru biyar da suka wuce!
Wannan ba gaskiya ba ne.