
Kungiyar matasan Jam’iyyar SDP sun bayyana cewa basu yadda da komawar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai Jam’iyyar ba.
Kungiyar ta bakin shugabanta, Abdulsamad Bello ta bayyana cewa, El-Rufai kawai yana son samun damar da zai cimma burinsa ne a Jam’iyyar.
Sun kara da cewa, abin takaici ne yanda Jam’iyyar ta baiwa El-Rufai dama aka tarbeshi hannu biyu-biyu ba tare da la’akarin hadarin da ke tattare dashi ba.
Matasan sun ce karamin misali shine yanda El-Rufai da ga zuwansa gashi yana son yayi kaka gida a Jam’iyyar har yayi yunkurin tsike sakataren Jam’iyyar, Dr. Olu Agunloye daga mukaminsa.
Kungiyar tace zata yaki duk wani yunkuri na neman mikawa El-Rufai Jam’iyyar inda suka gargadi shuwagabannin Jam’iyyar kada su aikata haka.