Friday, December 5
Shadow

Bani ba ku, bazan koma jam’iyyarku ta ADC ba>>Gwamnan Zamfara ya gayawa Su Atiku

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya nesanta kansa da maganar komawa jam’iyyar gamayyar ‘yan Adawa na ADC.

Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Zamfara, Kabiru Garba ne yayi kira ga gwamnan da ya koma jam’iyyar ta ADC amma Gwamnan yace sam ba zai koma ba.

Kabiru Garba a ranar Juma’a ne ya yin ganawa da manema labarai yacewa Gwamna Dauda Lawal Dare idan yana son sake cin zabe a shekarar 2027, to ya bar jam’iyyar PDP zuwa ADC.

Gwamnan ta bakin me magana da yawunsa, Mustafa Kaura ya bayyana cewa, babu abinda jam’iyyar ke dashi da zata amfanar dashi.

Dan haka zai ci gaba da zama a jam’iyyar sa ta PDP da kuma tabbatar da ci gabanta.

Karanta Wannan  Duk da kokarin da Gwamnatin Tinubu ta yi na rage farashin kayan abinci amma har yanzu gum kake ji babu me yabon shugaban kasar, sai ma ci gaba da zaginsa da ake yi>>Inji Wata kungiyar Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *