
Dajjito a masana’antar fina-finan Hausa, Isa Bello jaa ya bayyana cewa, kudin aikin fim basu kai suka kawo ba a yanda za’a ce mutum har zai iya mallakar wata kadara dasu ba.
An tambayeshi ne game da wanda ke sayen gidaje da motoci musamman ‘yan mata.
Malam Isa yace bai san wace harka suke yi suna samun wadannan kudade ba.
Yace amma su masu shirya fim din sukan samu Miliyoyin kudade a matsayin riba saboda kudi suka zuba suka shirya fim din.
Kalli Hirar da aka yi dashi a kasa: