Thursday, March 12
Shadow

Benjamin Hundeyin ya zama kakakin rundunar ƴansandan Najeriya

Babban Sifeton Ƴansandan Najeriya, Kayode egbetokun ya naɗa CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar ƴansandan ƙasar (FPRO)

Naɗin Hundeyin na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar.

‎”Babban Sifeton ƴansandan ya buƙace shi da aiki da ƙwarewarsa ta sadarwa wajen inganta aikin ɗansanda a Najeriya ta hanyar ƙarfafa hulda da jama’a,” in ji sanarwar.

Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasamnce kakain rundunar ƴansanda reshen jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana wannan aiki.

Karanta Wannan  Ji yanda kotu ta daure wata matashiya tsawon shekaru 7 ko ta biya tarar Naira Dubu dari hudu da hamsin bayan da Wani ya aika mata Naira Dubu 150 ta sameshi a gidansa amma ta cinye kudin kuma ta ki zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *