Bidiyon ‘yan kwallon Najeriya a filin wasan da suka buga wasa da kasar Africa ta kudu ya jawo cece-kuce.
Bidiyon ya nuna ‘yan kwallon na Najeriya sun ki rera sabon taken ko kuma ince sun kasa rerashi.
Saidai za’a iya cewa, har yanzu mutane da yawa basu kai ga iya taken ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya bayyana cewa, canja taken na daya daga cikin muhimman ayyukan da yake son yi a Najeriya.