Monday, January 13
Shadow

Abin Mamaki

Hoto: An kama mahaifi da yawa diyarsa me shekara daya fyàdè

Hoto: An kama mahaifi da yawa diyarsa me shekara daya fyàdè

Abin Mamaki
'Yansanda a jihar Anambra bisa hadin gwiwar kungiyar 'yanci sun kama wani magidanci me shekaru 46 bisa zargin yiwa diyarsa me shekara daya fyade. Mutumin me suna Christopher Ugwunna Azubuike An kamashi ne a kauyen, Uratta Amaogwugwu dake karamar hukumar Isialangwa North a jihar. Diyar tashi ita daya ce tilo suka haifa wadda ke da shekara 1 da watanni 9 da haihuwa bayan sun shafe shekaru 5 da yin aure. An kai yarinyar Asibiti kuma likitoci sun tabbatar da cewa an mata fyade. Wanda ake zargin yana hannun 'Yansanda kuma ana ci gaba da bincike.
Kalli Bidiyon yanda Wani Balarabe ke dukan bakar fata dake masa aiki a kasar Larabawa

Kalli Bidiyon yanda Wani Balarabe ke dukan bakar fata dake masa aiki a kasar Larabawa

Abin Mamaki
Bidiyon yanda wani balarabe ke dukan bakar fata ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda abin ya jawo Allah wadai. An ga yanda aka daure bakar fatar a kan kujera ana dukansa da sanda. Babu dai cikakken bayani kan dalilin faruwar hakan. https://twitter.com/AfricanHub_/status/1844466179865555302?t=41pQ3z9CjUPy2yj2zI_MhQ&s=19 Mutane da yawa daga kasashen Africa ne ke zuwa kasashe irin na larabawa da turawa dan neman abin yi.
Kalli Bidiyon wani Kìsàn Wulakanci da akawa wani bawan Allah da ya matukar tayar da hankulan mutane

Kalli Bidiyon wani Kìsàn Wulakanci da akawa wani bawan Allah da ya matukar tayar da hankulan mutane

Abin Mamaki
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani bidiyon kisan wulakanci da akawa wani bawan Allah ya tayar da hankula matuka inda aka ga an daure masa hannuwa an jefashi cikin Teku. Rahotanni dai sun bayyana cewa kungiyar masu harkar kwayane suka kama wani daga cikinsu da ya musu laifi shine suka masa wannan mummunan hukunci. https://twitter.com/newsxx0/status/1844346512626872350?t=qjeStu2S9u-ZVVJK0OqoSg&s=19 Mutane da dama dai sun yi Allah wadai akan wannan inda da yawa suke cewa rashin Imanine.
Matukin jirgin sama ya mutu yayin da yake tsaka da tukin jirgin a sararin samaniya

Matukin jirgin sama ya mutu yayin da yake tsaka da tukin jirgin a sararin samaniya

Abin Mamaki
Wani matukin jirgin saman Turkish Airlines ya mutu a yayin da yake tuka jirgin a sararin samaniya. Hakan yasa dole sauran matukan jirgin dake tare dashi suka karkatar da akalar jirgin zuwa birnin New York na kasar Amurka. Lamarin ya farune da safiyar ranar Laraba a yayin da jirgin ya tashi daga Seattle zuwa Istanbul. Matukin jirgin me suna Capt. İlçehin Pehlivan ya samu matsalar kidimewar gigin mutuwa yana tsaka da tuka jirgin. Saidai akwai sauran matuka jirgin 2 dake tare dashi inda suka yi gaggawar sauke jirgin a filin jirgi na John F. Kennedy International Airport dake birnin New York. Kamfanin jirgin ya tabbatar da cewa, Capt. İlçehin Pehlivan ya mutu ne kamin jirgin ya sauka kasa. Kamfanin ya kara da cewa lokaci na karshe da aka duba lafiyar Capt. İlçehin Pehlivan s...
Magidanci ya sayar da Dansa me watanni 11 kacal a Duniya ya buga caca da kudin

Magidanci ya sayar da Dansa me watanni 11 kacal a Duniya ya buga caca da kudin

Abin Mamaki
Wani magidanci ya sayar da dansa me watanni 11 kacal a Duniya inda yayi amfani da kudin wajan buga caca. Ya sayar da dan nasu ne ba tare da sanin matarsa ba. Lamarin ya farune a yankin Tangerang, West Jakarta na kasar Indonesia. Matarsa ta koma gida bata ga dan nasu ba inda ta tambayeshi, da ya fara mata kame-kame amma daga baya ya fito ya gaya mata gaskiya. Tuni 'yansandan 'yankin su suka kamashi. Ya dai sayar da danne akan farashin £730 kuma tuni suma wanda suka sayi dan aka kamasu.
Hotuna: Shahararriyar me nuna tsiraici ta musulunta

Hotuna: Shahararriyar me nuna tsiraici ta musulunta

Abin Mamaki
Wata shahararriyar me nuna tsiraici a kafafen sada zumunta, Brittany Renner ta musulunta. Ta bayyana cewa ta ga hasken musulunci ne shiyasa ta tuba dashiga addinin. https://twitter.com/brittanyrennerr/status/1820412139460349964?t=X1cA2NwpQ6EF63BAMrZ82g&s=19 A wasu hotunan ta da ta wallafa an ganta sanye da Hijabi maimakon kaya tsirara da aka saba ganinta dasu. A wani Bidiyo data wallafa kuma ta bayyana cewa har kayan sawarta ta canja.
Kalli Bidiyo:An kama Jami’in Hizbah a Kano cikin masu tallata aikin Lùwàdì da Màdìgò

Kalli Bidiyo:An kama Jami’in Hizbah a Kano cikin masu tallata aikin Lùwàdì da Màdìgò

Abin Mamaki
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an kama wani da ke ikirarin shi jami'in Hisbah ne dake tallata ayyukan luwadi da Madigo a jihar. Mutumin wanda yace sunansa, Idris Ahmad shine ke kula da bangaren kula da lafiya na Hisbah,kamar yanda yace. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1810342666774675604?t=hpiM9y6MP0wWVga3p1XMKw&s=19 An ganshi a wani Bidiyo yana bayyana cewa, 'yan Luwadi da Madigo suma mutanene kamar kowa kuma ya kamata a canja dokar data ce a rika hukuntasu har tsawon shekaru 14 da Gwamnatin tarayya ta saka. A lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne dai aka yi wannan doka inda yace ba zai amince da yarjejeniyar halatta Luwadi da Madigo ba. Saidai bayan yekuwa akan waccan magana da Idris Ahmad yayi, an kamashi. Bayan da aka kamashi, ya bayyanawa...