Monday, January 13
Shadow

Addu’a

Maganin kowace irin cuta

Addu'a, Ilimi
Babban maganin kowace irin cuta shine Qur'ani. Kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fada cewa: "Kuma mun saukar da qur'ani wanda warakane kuma rahama ne ga masu imani, amma ba zai amfani masu laifi da komai ba sai bata" Al-Isra’ 17:82. Wannan waraka na nufin ta zahiri da badili. Kamar yanda ma'aikin Allah, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallan) yake karanta suratul Falaq da Nasi akansa da iyalansa a yayin da suke fama da rashin Lafiya. Idan da hakan ba waraka bane, ba zai rika yi ba. Muslim (2192) ya ruwaito cewa, Matar Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasallam) A'isha ta ruwaito cewa, idan Annabi Muhammad( Sallallahu Alaihi Wasallam) bashi da lafiya, takan karanta masa Falaqi da Nasi ta shafa masa. Hakanan Muslim (2192) ya ruwaito cewa, Matar manzon Allah(SAW) A'...

Adduar yaye damuwa

Addu'a
Kana fama da yawan damuwa? Akwai addu'o'i wanda zaka iya yi wanda da yardar Allah zaka samu waraka. Na farko dai idan kana da lokaci, babban maganin damuwa shine karatun Al-Qurani, Musamman idan kasan fassarar abinda kake karantawa. Abu na biyu idan kai me yawan aiki ne ko baka cika samu ka zauna ba sosai. Akwai addu'a da zaka iya yi kamar haka: "La'ilaha illallahul Azimul hakim, la'ilahaillallahul hakimul karim, la'ilaha illallah, subhanallah, rabbussamawatis saba'i wa rabbul arshil azim, Alhamdulillahi Rabbil Alamin" Kai ta maimaitawa iya iyawarka, insha Allahu za'a samu warakar damuwa.

Addu’ar neman gafara ga mamaci

Addu'a
Idan za'a saka mutum a kabari, ana cewa, "Bismillahi, wa ala sunnati Rasulillah" Bayan an kammala binne mamaci, Annabi, Sallalalahu Alaihi Wasallam na cewa ku nemawa dan uwanku gafara. Kuma ku mai addu'ar samun nutsuwa, domin yanzu haka ana mai tambayoyi. Dan haka nemawa wanda ya rasu gafara da tabbatuwar harshensa akan gaskiya yayin tambayar kabari, Sunnah ce. Dan karin bayani, Saurari wannan bidiyon: Allah ya jikan wanda suka rigamu gidan gaskiya. Katanta: Yadda ake sallar gawaKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hutudole A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Addu’ar samun mijin aure da gaggawa

Addu'a
Ga me neman matar aure ko mijin aure, akwai addu'o'i da malamai na sunnah suka kawo wanda ke taimakawa wajan kawo nesa kusa. Addu'a ta farko itace Rabbana Atina Fidduniya hassana wafil Akirati Hassana, wakinna Azabannar. Wannan addu'a ta game kowace irin bukata mutum ke nema a Duniya da Lahira, kuma kusan duk musulmi ya santa amma wani yana ganin kamar ta yi kadan. Malaman Sunnah sun tabbatar da naci da yakini da sakankancewa ana wannan addu'a na kawo biyan bukata. Sai kuma Addu'a ta biyu. Itace "La'ilaha illallahul Azimul halim, La'ilaha illallahul hakimul Karim, La'ilahaillalah, Subhanallah, Rabbissamawatissaba'i wa rabbularshilazim, Alhamdulillahi rabbil alamin" Itama wannan addu'a idan aka haddace ta ana yinta akai-akai tana kawo nesa kusa. Akwai kuma addu'ar la'il...

Addu’ar samun kudi

Addu'a
Kana neman kudi dan aure, gina gida, sayen mota, gina babban gida daya fi wanda kake ciki, sayen kayan sawa, farantawa iyayenka, da dai sauransu? To ga addu'ar samun kudi daga bakin da baya karya, farin jakada, cikamakin annabawa da manzanni, Annabi Muhammadu, Sallallahu Alaihi Wasallam. Wannan addu'a an kawo ta a sunani Tirmizi, da Musnad na Imamu Ahmad. Addu'ar itace "Allahummagfirli Zambi Wawassi'ili fi daari, wa barikli fi rizqi Fassarar addu'ar itace ya Allah ka yafemin zunubaina, ka sa min nutsuwa a gidana, inji na wadata dashi, ka saka min albarka a Dukiyata. Allah ya Arzutamu Duniya da Lahira.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hutudole A shafin Facebook zaku samemu a @hutudole...

Wuridin kudi nan take

Addu'a
Musulunci ya amincewa mutum ya roki Allah Arzikin Duniya da ya hada da Kudi, Mata ta gari, da sauransu. Tirmizi ya ruwaito daga Sabit, Anas yace, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi waslalam yace "Kowannenku na da damar ya roki Allah dukkan abinda yake so, hadda rokon Allah madaurin takalmi idan ya katse. Albani ya inganta wannan hadisi. Wannan na nuni da cewa komai mutum zai roka ya roki Allah, saidai a nemi Albarka a cikin rayuwar Duniya da dukiyar da kuma Lahira zai fi. Hakanan manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam, ya taba tambayar Abuzar(RA) cewa, Abu Zar me kake tunani game da mutumin da yake da tarin Duniya, zaka kirashi me Arziki? Abu Zar(RA) ya amsa da cewa, tabbas zan kirashi da me Arziki ya Rasulullah. Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam ya sake tambayar ...

Addu’ar biyan bukata cikin gaggawa

Addu'a
Ga kuma kari: Wanda ya farka cikin dare, sai yace: "Lailaha illallah, Wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kullu shai'in qadir, walhamdulillah, wasubhanallahi, walailahaillallahu, wallahu akbar, wala haula wala quwwata illa billah" Sannan yace Allahummagfirli, ko yayi kowace irin Addu'a, Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallam yace Allah zai karba masa. Hakanan idan yayi Alwala yayi Sallah to za'a karbi sallarsa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hutudole A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole