fbpx
Friday, December 2
Shadow

Auratayya

Zinace-zinace na haifar da yawaitar mutuwar aure a Zambia

Zinace-zinace na haifar da yawaitar mutuwar aure a Zambia

Auratayya
Matsalar mutuwar aure a lardin gabashin Zambia na ƙaruwa cikin shekara biyu a jere, kamar yadda jaridar Zambia Daily taruwaito. Lardin shi ne cibiyar harkokin noma na ƙasar. A watanni takwas da suka gabata kimanin ma'aurata 3,400 ne suka shigar da neman a raba aurensu, a lardin. Kuma akasarin waɗanda suka shigar da buƙatar kashe auren sun kafa hujja ne da zargin zina a ɓangaren mijin ko kuma matar. A bara an samu mutuwar aure 4,441 ne, amma an yi hasashen cewar mace-macen auren na bana zai zarta na shekarar da ta gabata. Sauran dalilan da ke haifar da mutuwar auren sun haɗa da cin zarafin abokin zama da kuma zaluntar juna. Jaridar ta ce a kashe aurarraki da dama a yankin domin kauce wa cin zarafin juna da ke iya kai wa ga kisan kai.
Ta Rasu Ana Gobe Aurenta

Ta Rasu Ana Gobe Aurenta

Auratayya
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Daga Nuruddeen Isyaku Daza Bincike ya nuna cewa a gobe ne aka sa ranar auren marigayiya Maryam da angon ta Yunus, a garin Ofa dake Jihar Kwara amma yau tace ga garin ku nan bayan fama da 'yar gajeruwar jinya. Muna fata Allah yayi mata mahama.
Kasashen da mata ke auren maza fiye da daya

Kasashen da mata ke auren maza fiye da daya

Auratayya
A yayin sa al'ada da addimi yawanci ansan maza ne ke auren mata fiye da daya. Akwai kasashen Duniya da suka halattawa mace ta auri maza da yawa.   Kasar India.   Akwai yankuda da yawa a kasar Indiya dake amincewa mata auren maza fiye da daya, wasu daga cikinsu sune: Jaunsarbawar   Akwai kuma kabilar Nilgiris data Najanad Vellala da suma ke wanan kazantar, hakanan a Tibet ma an samu mata masu auren maza fiye da daya.   Kenya. A kasar Kenya ma an samu rahotannin auren maza fiye da daya da mata keyi.   An samu rahoton farko ne a shekarar 2013. Inda kuma daga nan kofa ta bude.   Kasar China. A kauyukan kasar China an samu rahotannin mata na auren maza da yawa, saidai wannan al'ada ba a yinta a biranen kasar.   ...
Dalilan Da Suka Sa Ake Ganin Auren Bazawara Ya Fi Na Budurwa Inganci

Dalilan Da Suka Sa Ake Ganin Auren Bazawara Ya Fi Na Budurwa Inganci

Auratayya
Daga Hajiya Mariya Azare Bazawara dai ita ce matar auren da suka rabu da mijinta sandin mutuwa ko kuma rabuwa. Budurwa kuma ita ce wacce ba ta taba yin aure ba. Mafi yawan samari ba su son auren bazawara, amma masana sun yi nuni da cewa, akwai fa'idoji da dama a cikin aurenta. Ga dalilan masana kamar haka; 1. Za ka samu ladan sunna idan ka yi, domin ka yi koyi da Fyayyen Halitta SAW. 2. Auren macen da ta fi ka shekaru, akwai yiyuwar samun ingantacciyar rayuwar aure matukar akwai soyayya. 3. Hakika bazawara ta fi budurwa sanin makaman aiki a zamantakewar aure musamman ma idan ta samu saurayi wato wanda ta girma. 4. Bazawara tana hakurin zamantakewa fiye da budurwa domin ita budurwa ta kware wajen yaudara. 5. Bazawara ko wadda ta fi ka shekaru ta san halayen iy...
Malamin makarantar nan me ‘ya’ya 18, ya samu karuwar da na 19 sannan ya kara aure

Malamin makarantar nan me ‘ya’ya 18, ya samu karuwar da na 19 sannan ya kara aure

Auratayya
Malamin makarantar Umar Bin Khattab dake Unguwar Tudun Nupawa a jihar Kaduna wanda yayi suna saboda yawan 'ya'yansa 18, ya samu karin haihuwar da na 19.   Sannan malamin ya auri mata ta 4.   Da babbar sallah ne dai malam Mohammed Sulaiman ya fito idon Duniya inda aka ga hotunansa da iyalinsa.   Ranar 1 ga watan October, malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, ya samu karuwar da namiji, sannan ya kara aure, hakanan kuma ya aurar da diyarsa.  
Wata mata ta maka mijinta a kotun Shari’a dake Kaduna ta bukaci ya sallameta domin yana nemanta a cikin watan Ramadana da lokutan al’adarta

Wata mata ta maka mijinta a kotun Shari’a dake Kaduna ta bukaci ya sallameta domin yana nemanta a cikin watan Ramadana da lokutan al’adarta

Auratayya, Breaking News
Wata mata Zainab Yunusa ta maka mijinta Garba a kotun Shari'a dake Magajin Gari a Kaduna inda ta bukaci ya sallameta saboda yana nemanta a lokutan da basu dace ba. Zainab ta bayyana cewa mijin nata yana nemanta a lokutan data ke yin al'ada sannan kuma hatta a cikin watan Ramadana baya raga mata wanda hakan kuma ya sabawa koyarwar addinin Musulunci. Sannan tace yana hanata abinci kuma baya barin danginta suna kai mata ziyara, saboda haka ne take rokar kotun ta umurce shi ya sallameta, amma shiya karyata wannan korafin nata. Yace karya take yi kuma kafin ta gudu a gidansa ita da mahaifiyarta sun sayar masa da kayayyakinsa, wanda hakan yasa alakali yace tazo da mahaifiyarta a ranar 27 ga watan satumba domin a cigaba da sauraron wannan shari'ar.