Friday, January 10
Shadow

Duk Labarai

Hotunan muggan makamai na Naira Biliyan 13.9 da hukumar Kwastam ta kama za’a shigo dasu Najeriya

Hotunan muggan makamai na Naira Biliyan 13.9 da hukumar Kwastam ta kama za’a shigo dasu Najeriya

Duk Labarai
Hukumar kula shigar kaya da fitarsu daga cikin Najeriya, Kwastam ta kama wasu muggan makamai na Naira Biliyan 13.9 a jihar Rivers. An kama makaman tare da harsasai da kayan sawa na gwanjo da miyagun kwayoyi. https://twitter.com/MobilePunch/status/1807827328887623905?t=tCzC8zaWQO6I6aoYlTeuUA&s=19 Shugaban hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da yayi ranar Litinin.
Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Ta Rasu

Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Ta Rasu

Siyasa
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN. Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Ta Rasu Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Tsohan Gwamnan Jihar Borno, Hajia Aisa Modu Shariff Rasuwa A Wata Asibiti Dake Abuja, Yau Lahadi Tana Da Shekara 93 A Duniya. Za'a Yi Jana'izarta Gobe Litinin Bayan Kammala Sallar Azahar A Gidan Marigayi Galadima Modu Shariff Dake Kan Hanyar Damboa, Maiduguri Jihar Borno. Allah Ya Jikanta Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa

Amfanin ridi da madara

Duk Labarai
Amfanin ridi (sesame) da madara (milk) yana da yawa ga lafiyar jiki. Ga wasu daga cikin amfanin su: Amfanin Ridi: Yana ƙara ƙarfin ƙashi: Ridi yana ɗauke da sinadarin calcium da ke taimakawa wajen gina ƙashi masu ƙarfi. Yana taimakawa wajen rage ƙiba: Yana ƙunshe da sinadaran fiber da antioxidants da ke taimakawa wajen rage nauyi. Kariya daga cututtuka: Ridi yana da sinadarai masu yawa da ke taimakawa wajen kariya daga cututtuka kamar su cutar zuciya da ciwon suga. Yana da sinadarin Vitamin E: Wannan sinadari yana taimakawa wajen inganta fata da kuma ƙwayoyin jiki. Amfanin Madara: Ƙara ƙarfin ƙashi da hakora: Madara tana da sinadarin calcium da ke taimakawa wajen gina ƙashi da hakora masu ƙarfi. Ƙara ƙarfin garkuwar jiki: Madara tana da sinadarin Vitamin D da...
Yawan wanda suka mutu bayan harin kunar bakin wake sun kai 30, guda 100 sun jikkata a jihar Borno

Yawan wanda suka mutu bayan harin kunar bakin wake sun kai 30, guda 100 sun jikkata a jihar Borno

Borno, Tsaro
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, yawan wadanda suka mutu ya karu zuwa 30 daga 8 da jami'n tsaro suka bayyana a jiya. Hakanan yawan wadanda suka jikkata ya karu zuwa 100. Rahoton jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta ya tabbatar da faruwar lamarin. Jaridar tace Timta ya bayyana mata cewa 'yar kunar bakin wake ta farko ta je wajan bikine tare da yara inda ta tayar da bam sannan an samu ta biyu itama taje wajan wani bikin ta sake tayarwa. Timta ya kara da cewa, an sake samun wani tashin bam din a karo na 3. A baya dai, jaridar Premium times ta ce 'yan kunar bakin wake 4 ne suka tayar da bamabamai a Garin na Gwoza. Timta dai yace ba'a kammala samun bayanai ba amma zuwa yanzu mutum 100 sun jikkata kuma an garzaya da wasu zuwa Maiduguri.
Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba’a gano inda take ba

Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba’a gano inda take ba

Katsina, Rarara, Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, awanni 24 bayan yin garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, Rarara har yanzu, ba'a gano inda take ba. Kakakin 'yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa an kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da mahaifiyar Rarara din amma har yanzu ba'a gano inda take ba. Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan Bindigar da suka je yin garkuwa da mahaifiyar Rarara sun je ne a kafa tike da muggan makamai suka shiga gidanta suka kamata. Rahoton yace Bata musu gaddama ba kuma babu wanda ya tunkaresu saboda muggan makaman da suke dauke dasu. Daily Trust tace ta nemi jin ta bakin Rarara amma bata yi nasara ba saboda wayoyinsa duk a kulle kuma an aika masa da sakon waya amma bar bayar da amsa ba.
Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban da ba'a taba yin irinsa ba wajan jajircewa da yiwa Najeriya aiki. Ya bayyana hakane jiya kamar yanda jaridar thisday ta bayyana. Yace shugabanci ba da karfin jiki ake yinsa ba, da kaifin tunani ake yinsa dan haka a daina alakanta lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin da yake. Ya kuma yi Allah wadai da wadanda suka rika yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dariya a ranar Dimokradiyya data gabata.

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 8 a Maiduguri da jikkata wasu da dama

Borno, Tsaro
Rahotanni daga jihar Borno na cewa harin Bom ya kashe akalla mutane 8 da jikkata mutane da dama. Harin wanda na kunar bakin wakene mahara 4 ne suka kaishi kuma rahoto yace dukansu sun mutu. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da mutane 8 ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya bayyana cewa lamarin ya farune da misalin karfe 3:40 na safiyar yau,Rabar, 29 ga watan Yuni. Rahoton yace wata mata dake goye da yaro ta tayar da bom din a tashar motar Mararraba dake T. Junction dake garin Gwoza. Matar da dan da take goye dashi da wasu 6 sun mutu. A bangaren jaridar Premium times kuwa, tace mata 4 ne suka tayar da bamabamai a bangarori daban-daban na jihar wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba'a kai ga tantance yawansu ba c...
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

labaran tinubu ayau, Siyasa
Cire harajin ya shafi kayan asibiti da suka haɗa da magunguna na ƙwayoyi da na ruwa, sirinji da allurai, sanke na rigakafin cizon sauro, abubuwan gwaji na gaggawa, da sauran kayan amfani a asibiti na yau da kullum. Hakazalika, umarnin na shugaban ƙasa zai ƙara ƙarfafawa masana'antun sarrafa magunguna da kayan asibiti na cikin gida wajen kara inganta su da samar da su a wadace. Wannan zai rage farashin magunguna da kuma wadatar su a lunguna da saƙon kasar nan don amfanin ƴan Najeriya.