Friday, January 10
Shadow

Duk Labarai

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

labaran tinubu ayau, Siyasa
Gwammatin tarayya a karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen da shugaban kasar ke amfani dasu a cikin watanni 11 da suka gabata. Hakan na zuwane a yayin da majalisar tarayya ta amince a sayowa shugaban kasar sabbin jirage 2. Kudin da za'a kashe wajan siyo sabbin jiragen sun kai Naira Biliyan 918.7 ko kuma dala Miliyan 623.4, kamar yanda kwamitin majalisar ya bayyana. Rahotanni dai sun bayyana cewa, jiragen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima ke amfani dasu sun tsufa sosai suna bukatar a canjasu.
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja

Duk Labarai
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya, FCT, ta kaddamar da bincike kan wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wani Birgediya Janar na sojojin Najeriya, Uwem Harold Udokwe mai ritaya. DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe Janar Udokwe a babban birnin kasar ranar Asabar. Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an kai wa marigayin hari tare da kashe shi a gidansa na Sunshine Homes Estate da misalin karfe 3 na safiyar ranar Asabar. Ta ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth C. Igweh, “ya ​​ba da umarnin gudanar da sahihin bincike kan al’amuran da ...
Kalli Bidiyo: Yanda matasa suka yi mummunan hàdàri a Jalingo saboda tukun ganganci

Kalli Bidiyo: Yanda matasa suka yi mummunan hàdàri a Jalingo saboda tukun ganganci

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wasu matasa da suke tukin ganganci a Jalingo na jihar tarabawa sun yi hadari inda motarsu ta juya. Bidiyon faruwar lamarin ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda akai ta musu Allah wadai, wasu kuma na musu jaje. Saidai babu wanda ya rasu amma dai an ji raunika.
An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

An Gudanar Da Addu’ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa

labaran tinubu ayau, Siyasa
An Gudanar Da Addu'ar Cikar Mahaifiyar Shugaba Tinubu Shekaru Sha Daya Da Rasuwa …wanda shugaban hukumar kula da almajirai ta kasa ya jagoranta a yau Juma'a Daga Mustapha Narasulu Nguru Shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta na kasa, Dr. Muh'd Sani Idriss Phd ya jagoranci addu'a ga mahaifiyar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu GCFR, wanda aka gabatar yau Juma'a. Shugaban hukumar ya yi addu'a a gare ta sosai a yau Juma'a 21/06/2024 a yayin da take cika shekaru sha daya da barin duniya. Cikin jawabansa ya rokar mata rahama ga Allah (SWT) kamar yadda addini ya tanadar. Muna fatan Allah Ya yi mata rahama da sauran y'an uwa musumal. Allah Ya sa Aljannah makoma.
Ji tsokanar da dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi yawa Tsohon Gwamnan Kano, Ganduje

Ji tsokanar da dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi yawa Tsohon Gwamnan Kano, Ganduje

Kano, Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Bayan hukuncin kotu kan rushe sabbin masarautun Kano, lamarin ya jawo cece-kuce a jihar inda mahawara ta yi zafi kuma kowane bangare tsakanin gwamnatin Kano, da Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero ke ikirarin yin nasara, Gwamnatin jihar ta sa a rushe gidan sarki na Nasarawa wanda sarki Aminu ke ciki. A wasu hotuna da bidiyo da suka watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga yanda motocin rushe gida suka je fadar ta Nasarawa. Yayin da yake mayar da martani akan wannan lamari, dan gidan Sarki Muhamma...
Shugaba Tinubu ya saka jiragensa 3 a kasuwa

Shugaba Tinubu ya saka jiragensa 3 a kasuwa

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta sanar da saka jiragen shugaban kasar guda 3 a kasuwa dan sayarwa. Jiragen dai sun tsufane shine aka tattara za'a sayar dan samun kudaden da za'a siyo sabbi. Wannan mataki kuma zai rage kudaden da ake kashewa wajan kula da jiragen wanda ba duka Shugaban kasar ke amfani dasu ba. Hakan na zuwane yayin da majalisar tarayya ta bada shawarar saiwa shugaban kasar da mataimakinsa sabbin jirage.
Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

Duk Labarai
'Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da satar mota kirar Toyota Corolla. Kakakin 'yansandan na Abuja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da lamarin inda yace an kamasu ne ranar Juma'a. Yace an kamasu ne a yayin da suke kokarin sayar da Motar a kan Naira Miliyan 6.5 a Minna. Wadanda aka kama din sune, Gwaza Bulus san kimanin shekaru 41 da kuma Yahya Amodu dan kimanin shekaru 45. Ana ci gaba da bincike kan lamarin.