‘Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi’
Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya zargi 'yan ƙasar a kan fifita siyasar kuɗi maimaikon zaɓar mutane masu aƙidar da za su iya kawo canji.
Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce dimokraɗiyyar Najeriya ta samu koma-baya saboda wasu 'yan siyasa da kan sayi ƙuri'un mutane ta hanyar ba su atamfa ko taliya.
A cewarsa, irin wannan tunani na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jefa al'ummar ƙasar cikin halin matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaron da hukumomi suka gaza shawo kansu ya zuwa yanzu.
Ya kuma ce rashin iya mulki ne ya haddasa taɓarɓarewar al'amura kamar tsaro da tattalin arziƙi a Najeriya.
Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana haka a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu ƙusoshin siyasar Nijeriya a wani ɓangare na cika shekara 25 da mulkin dimokraɗiyya karon...