Wani dan Arewa ya karyata Hukumar sojojin Najeriya bayan da suka yi ikirarin kubutar da dan uwansa daga mutanen daji.
Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da kubutar da wasu mutane daga daji inda ta wallafa hotunansu a shafinta na sada zumunta.
Saidai matashin me suna Abdullahi Kamba ya hangi dan uwansa cikin wadanda aka ce an kubutar inda yace wallahi karyane.
Ya bayyana cewa sai da suka bayar da kudin fansa hadda mashin.
https://twitter.com/i/status/2067234583247049053
Ganin dan takarar jam'iyyar APC a jihar Ekiti na jefawa mutane Burodi daga mota su kuma mutane suna bi suna wawa ya jawo cece-kuce sosai.
A ranar Asabar ne dai za'a gudanar da zabe a jihar Ekiti.
https://twitter.com/i/status/2067877463300952247
Ko da a jiya, sai da aka ga wasu ana basu Indomie da tumatur na leda a wajan yakin neman zabe a jihar ta Ekiti.
Bidiyo ya bayyana na ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike inda aka ga yana gaisawa da wasu 'yan kasar China a wajan taro.
Saidai yaki gaisawa da 'yan Najeriya inda lamarin ya jawo masa suka.
https://twitter.com/i/status/2067873105121341710
Wannan wani matashi ne da aka kama yawa kanwarsa cikin shege.
A Bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta, an ga kanwar tasa da ciki inda take bayar da labarin yanda abin ya kasance.
Saidai matashin ya rika rokon a dauna daukarsa Bidiyon.
https://twitter.com/i/status/2067858734408245350
Farashin dala a kasuwar Chanji ta gwamnati a yau, Juma'a, 19 ga watan Yuni, ya kamane akan Naira ₦1,360/$ akan kowace dala.
Farashin ya dan yi rawa a tsakanin Naira ₦1,357 zuwa Naira ₦1,364.
Farashin a kasuwar bayan fage kuwa yana tsakanin Naira ₦1,390 zuwa Naira ₦1,400, ya danganta mutum idan saye ko sayarwa zai yi.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta cire naira Biliyan 500 daga asusun hadakar Gwamnatoci kamin a raba kudaden shigar da aka tare tsakanin Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi.
Wata Majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng cewa lallai an cire kudin wanda aka ware dan ko ta kwana musamman a bangaren tsaro.
Jaridar tace akawun jihohi wanda dasu ake aikin raba wadannan kudade basu yi korafi akan cire wadannan kudade ba wanda hakan ke nuna cewa suna sane da hakan.
A baya ma dai an cire jimullar Naira Biliyan N952bn inda aka baiwa Sojoji, da wasu ma'aikatun Gwamnati da yin ayyukan ci gaba a wasu jihohi.
Gwamnatin tarayya ta gargadi gidajen Jaridu da cewa, su daina yada labaran tsageran daji.
Hakan ya fito ne daga bakin ministan yada labarai Muhammad Idris a wajan wani taro da aka shirya da hadin gwiwar hukumar DSS da kafafen watsa labarai.
Yace abin yana bashi takaici yaga shafukan farko na jaridun Najeriya na magana akan harkokin mutanen Daji yayin da ba'a son watsa nasarorin sojoji.
Yace wannan abu na watsa labarin abinda tsageran daji suke yi su dama abinda suke son a yi kenan gashi kuma ana musu shi kyauta.
Yace ya kama masu kawo rahoto da masu tacewa su san labarin da ya kamata a yada da wanda bai kamata a yada ba dan tsaro da ci gaban kasa.
Wannan Baturiyar kasar Ingila ce me shekaru 68 wadda a karin farko ta hadu da Saurayinta me shekaru 27 dan Najeriya da suka dade suna chating
Lamarin ya dauki hankula.
https://twitter.com/i/status/2067568932630777961