Sunday, February 22
Shadow

Duk Labarai

Kamin In Auri Gfresh Har ce min Aka yi Zàrmàlùlùnsà ba ta aiki amma na rufe ido na aureshi, kuma na zauna dashi tun bashi da komai har ya samu budi ya Koma Abuja>>Inji Matar Gfresh Maryam

Kamin In Auri Gfresh Har ce min Aka yi Zàrmàlùlùnsà ba ta aiki amma na rufe ido na aureshi, kuma na zauna dashi tun bashi da komai har ya samu budi ya Koma Abuja>>Inji Matar Gfresh Maryam

Duk Labarai
Matar Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin, Maryam ta bayyana cewa, Tun bashi da komai ta aureshi. Ta bayyana cewa haka ta zauna dashi har ya samu budi ya koma Abuja da zama. Ta kara da cewa kuma kamin ta aureshi har ce mata aka yi Zarmalulunsa baya aiki amma haka ta rufe ido ta aureshi amma yanzu ya wulakantata. Ta yi gargadin cewa, a wannan fadan da suke duk wanda ya kara kafeta yana cewa laifinta ne ko ita ce me laifi saita ci Kutumar Bura Ubansa. https://www.tiktok.com/@amanaatamama2/video/7576069185340460300?_t=ZS-91fG76B7bjF&_r=1
Kalli Sabon Bidiyon da Sadiya Haruna ta Wallafa inda tace Zawarci ba Dadi ita shaida ce, Sannan ta fashe da dariya

Kalli Sabon Bidiyon da Sadiya Haruna ta Wallafa inda tace Zawarci ba Dadi ita shaida ce, Sannan ta fashe da dariya

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Sadiya Haruna ta wallafa Bidiyo inda ta saka wakar Ko yau Kasuwa ta watse. Sannan ta bayyana cewa zawarci ba dadi domin ita shaida ce Da aka Mata maganar ta raba auren Gfresh da matarsa Maryam kuwa, fashewa ta yi da dariya. https://www.tiktok.com/@sayyada_sadiya_haruna/video/7576216580007169336?_t=ZS-91fDCXuxWMr&_r=1
Kalli Bidiyon: Satin ta daya da fara aiki, Wani ya je ya bata kyautar Naira Dubu 60, Yayin da Albashinta Naira Dubu 50 ne, Oganta ya nuna bacin rai

Kalli Bidiyon: Satin ta daya da fara aiki, Wani ya je ya bata kyautar Naira Dubu 60, Yayin da Albashinta Naira Dubu 50 ne, Oganta ya nuna bacin rai

Duk Labarai
Wani me shagon sayar da kayan sawa ya nuna bacin ransa sosai bayan da sabuwar ma'aikaciyar da ya dauka aiki ta samu kyautar Naira Dubu 60 daga wani da ya je shagon. Yace satin ta biyu kacal da fara aiki a shagon kuma Albashin Naira dubu 50 yake biyanta. A Bidiyon an ji kuma yana cewa, wani ma ya fara sai mata abinci. Lamarin dai ya jawi muhawara kan aiki da irin wadannan abubuwan dakan dauke hankalin ma'aikata. https://twitter.com/CryptoEth1969/status/1992477832266875379?t=00nf-McXsQxQX-B7ac379w&s=19
‘Yansanda 5 sun Rigamu Gidan Ghàskìyà bayan Khàrìn Kwantan Bauna a jihar Bauchi

‘Yansanda 5 sun Rigamu Gidan Ghàskìyà bayan Khàrìn Kwantan Bauna a jihar Bauchi

Duk Labarai
' Yansandan Najeriya 5 ne suka rigamu gidan gaskiya bayan Harin Kwantan Bauna da aka Afka musu a jihar Bauchi. Lamarin ya farune a kauyen Sabon-Sara dake karamar hukumar Darazo ta jihar inda aka kira 'yansanda dan su kawo dauko kan rikicin makiyaya da manoma. Saidai bayan isarsu wajan wasu 'yan Bìndìgà sun Afka musu da hari inda aka Khashye 'yan Bìndìgàr da yawa. Daidai 'yansanda 5 ma sun rasa rayukansu. Wadanda suka rasa rayukan nasu sune : DSP Ahmad Muhammad (SID) ASP Mustapha Muhammad (10 PMF) Inspector Amarhel Yunusa (10 PMF) Inspector Idris Ahmed (10 PMF) Corporal Isah Muazu (AKU)
Shugaba Tinubu ya sa a janye ‘yansanda daga tsaron manyan mutane a kasarnan, yace duk wani babban mutum dake neman tsaro a bashi jami’an Civil Defence

Shugaba Tinubu ya sa a janye ‘yansanda daga tsaron manyan mutane a kasarnan, yace duk wani babban mutum dake neman tsaro a bashi jami’an Civil Defence

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a janye jami'an 'yansanda dake baiwa manyan mutane tsaro a fadin Najeriya. Shugaban yace duk wani babban mutum dake neman jami'an tsaro a bashi jami'an Civil Defence. Shugaban ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda jami'an 'yansandan dake a ofisoshin 'yansanda dake Fadin Najeriya sun yi kadan. Hakanan yace duk 'yansandan za'a mayar dasu wajan aikin da shine dama ya kamata suna yi. Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan taron da shugaba Tinubu yayi da shuwagabannin jami'an tsaro na kasa ranar Lahadi. Sannan yace shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a dauki sabbin jami'an 'yansanda guda dubu 30.
Idan muka bi ka ta lalama kaki yadda ka biyan kudin Haraji, zamu iya kwasa kawai daga Asusun Ajiyar ka ta banki>>Inji Gwamnatin Tarayya

Idan muka bi ka ta lalama kaki yadda ka biyan kudin Haraji, zamu iya kwasa kawai daga Asusun Ajiyar ka ta banki>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa sabuwar dokar Haraji ta tanadi tsarin da zai nunawa Gwamnati yanda mutum ke kashe kudinsa. Ta wannan hayar ne Gwamnatin zata san ainahin yawan kudin shigar mutum. Shugaban kwamitin shugaban kasa akan Haraji, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi. Yace za'a bukaci mutum ya bayyana nawa yake samu kudin shiga a Shekara, amma idan mutum yayi Qarya, zasu gani ta hanyar yawan kudaden da yake kashewa. Yace ta nan ne zasu fahimta kuma su nemi mutum ya biya kudin Haraji, yace idan mutum ki biya, zasu iya diba daga cikin asusun ajiyarsa na banki ba tare da an yi wani rikici dashi ba. https://twitter.com/OneJoblessBoy/status/1992540377228927482?t=HrKNFcUoyNAIFmu9J155Sw&s=19
Ta Shyekye Mijinta a Jibiya jihar Katsina, Kwana uku bayan an daura musu aure

Ta Shyekye Mijinta a Jibiya jihar Katsina, Kwana uku bayan an daura musu aure

Duk Labarai
INNA LILLAHI WA'INNA ILAHI RAJI'UN: Ta Ýi Wà Mìjìɲțà Yàñkàñ Rãģø Bayàñ Kwanà Ukù Da Ɗauriɲ Aųrèɲșù A Kãțșiɲà Wannan da kuke gani sunansa Abubakar Ɗan Gaske Mai Nasara, ɗan garin Jibia ne dake jihar Katsina, yau kwana uku da daura auren su tare da wannan matar ta sa mai suna Aisha Muhammad, sai ga shi a jiya Lahadi 23/11/2025 yana cikin bacci da rana a gida tà sà wùķã tà ýì mãśà ýªªɲķàñ řªğø. Allah Ya gafarta masa. Daga Dokin Karfe.
Kalli Bidiyon: Labarin yanda wani gari a Katsina suka dauke iyalan Tshàgyèràn Dhàjì bayan da suka yi Ghàrkùwà da ‘yan uwansu

Kalli Bidiyon: Labarin yanda wani gari a Katsina suka dauke iyalan Tshàgyèràn Dhàjì bayan da suka yi Ghàrkùwà da ‘yan uwansu

Duk Labarai
Wannan bawan Allahn ya bayar da labarin yanda Mutanen Sabon Birni dake jihar Katsina suka sace iyalan Fulani 'yan Bindiga bayan da Fulanin suka yi garkuwa da iyalansu. Ya bayyana cewa, Fulanin sun nemi a yi Sulhu inda mutanen garin Sabon Birnin suka ce musu kawai su sako ya saki iyalan kowa. Ya bayyana cewa, 'yan Bindigar bayan sun saki mutanen kauyen sun basu hadda kudin motar zuwa gida. https://twitter.com/OurFavOnlineDoc/status/1992823277174333566?t=o83vIwYzeMsRZuxTI2kzew&s=19
Kalli Bidiyon: Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Ibrahim El-Rufai, sanye da Dan Kunne, Yayi Kitso, sannan yace yana saka Sarqa da Barimar hanci ya dauki hankulan mutane

Kalli Bidiyon: Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Ibrahim El-Rufai, sanye da Dan Kunne, Yayi Kitso, sannan yace yana saka Sarqa da Barimar hanci ya dauki hankulan mutane

Duk Labarai
Dan gidan Tsohon Gwamna Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai me suna Ibrahim El-Rufai ya dauki Hankula sosai a kafafen sada zumunta bayan ganinsa da kitso da Dankunne. Ya bayyana cewa yana kuma saka Sarqa da Barimar Hanci. A Bidiyon da ya saki a shafinsa yace bashi da wata alaqa da mutanen Arewa dan haka su fita a rayuwarsa su daina bibiyarsa a shafin sa na sada zumunta. https://www.tiktok.com/@nigeria_gossip_club/video/7576052800006753556?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7576052800006753556&source=h5_m&timestamp=1763986688&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&...
Kalli Hotuna: Yanda Kiristoci musamman ‘yan Kudu ke suka fara zuwa coci da Bìndìgù saboda fargabar Kharin Tshàgyèràn Dhàjì

Kalli Hotuna: Yanda Kiristoci musamman ‘yan Kudu ke suka fara zuwa coci da Bìndìgù saboda fargabar Kharin Tshàgyèràn Dhàjì

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Kiristoci daga kudancin Najeriya sun fara sayen Bindigu saboda kariyar kai daga hare-haren Tshàgyèràn Dhàjì. Da yawa sun rika wallafa hotunan Bindigun nasu a kafafen sada zumunta inda suke cewa lamarin hare-haren 'yan Bindigar Dhajin yayi yawa. A Lahadin data gabata, wasu sun nuna yanda suka rika daukar Bindingun zuwa coci: https://twitter.com/dammy_jegz/status/1991157208717885949?t=fYPb2iBV5ZaWZwwAAVzNWQ&s=19 https://twitter.com/Amb_Honesty/status/1991519632033972524?t=DAVgUTAa7Ug9D323RDelGg&s=19 https://twitter.com/UrfavBoyq/status/1991984310702985686?t=njc2USUaoIzDJ9XZNIUiLg&s=19 https://twitter.com/vibe_cityy/status/1992553341029683644?t=F5-gbiUbkZvzV95t8GtG6A&s=19 https://twitter.com/99_ment...