Monday, November 23
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon Yanda ICPC suka hana Iyalan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bashi Abinci

Kalli Bidiyon Yanda ICPC suka hana Iyalan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bashi Abinci

Duk Labarai
Hukumar ICPC ta hana iyalan Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bashi abinci. Matarsa Aisha ce ta bayyana haka a wani Bidiyo data wallafa a kafafen sada zumunta inda tace gata ta zo kaiwa mijin nata abinci amma ICPC sun hanata ta bashi. Hakanan Dansa, Hon. Bello El-Rufai ya tabbatar da hakan inda yace antinsu ta kaiwa babansu abinci a ofishin ICPC kamar yanda ta saba da yamma amma aka hanata shiga inda aka ce an hana shigar masa da abinci idan yamma ta yi. Hakanan yace Likitansa ma ya je ganinsa aka hanashi ganinsa. Yace wannan take hakki ne wanda bai kamata ba. Ya bayyana cewa suna neman a dawowa da babansu hakkinsa na dan Adam kamar yanda kundin tsarin Mulkin Najeriya ya bashi dama. https://twitter.com/i/status/2055396738496606522
Kalli Bidiyon: Yanda Adam Garba(Raba Gardama) da tsohuwar matar Adam A. Zango, Ameena suke ta taba juna a wani fim ya dauki hankula

Kalli Bidiyon: Yanda Adam Garba(Raba Gardama) da tsohuwar matar Adam A. Zango, Ameena suke ta taba juna a wani fim ya dauki hankula

Duk Labarai
Bidiyon wani sabin Fim da Adam Garba, wanda aka fi sani Raba Gardama da tsohuwar matar Adam A. Zango, Ameena suka fito a ciki ya dauki hankula sosai. Dalili kuwa shine an ga suna yin abubuwan da ba'a aaba gani ba a fina-finan Hausa, watau suna ta taba juna. Wasu dai sun rika tambayar shin An daina tace fim din Hausa ne? Inda wasu ke tambayar ko kuwa a mahaukaciya ta fito a film din. https://www.tiktok.com/@rrproduction2026/video/7639874239390174485?_r=1&_t=ZS-96OEo3S5Tj2
Bidiyon mahajjata daga Jihar Adamawa suna kwana a waje a kasar Saudiyya ya dauki hankula

Bidiyon mahajjata daga Jihar Adamawa suna kwana a waje a kasar Saudiyya ya dauki hankula

Duk Labarai
Mahajjatan jihar Adamawa da suka je kasar Saudiyya sun rasa dakunan kwana inda aka gansu suna kwana a waje. Da yawa da aka yi hira dasu sun bayyana cewa basu da daki kuma suna neman hukumomin jiharsu dana kananan Hukumomin su amma basu gansu ba. An ji wanda ya dauki Bidiyon hana kokawa cewa ya kamata a dauki matakin da ya dace. https://twitter.com/i/status/2054860996850696454
Biyo bayan cewar da yayi ya samawa mutane aiki>>An zakulo tsohon Bidiyon Hon. Isa Ali Pantami inda yake cewa, A matsayinsa na Minista ba zai iya samarwa kowa aiki ba

Biyo bayan cewar da yayi ya samawa mutane aiki>>An zakulo tsohon Bidiyon Hon. Isa Ali Pantami inda yake cewa, A matsayinsa na Minista ba zai iya samarwa kowa aiki ba

Duk Labarai
A wata hira da Farfesa Hon. Sheikh Isa Ali Pantami yayi da gidan Talabijin na Trust TV ya bayyana cewa ya samarwa mutane aiki inda ake biyansu Albashi me tsoka Akwai zarge-zargen cewa, Farfesa Isa Ali Pantami bai samawa mutane da yawa ayyukan yi ba a matsayinsa na Minista lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Saidai malam yace Ba yawan aikin bane, ingancin aikin ake bukata. Ya bayyana cewa,mutum daya daya kirashi yake masa godiya, yace masa aikin da ya samar masa ana biyansa Albashin Miliyan 80 a shekara. Saidai a yanzu kuma An zakulo wani tsohon Bidiyon malam innda yake cewa a matsayin sa na Minista, ba zai iya samarwa da kowa aiki ba. Hakane yasa wasu suka zargi malam da Tubka sa warwara. https://twitter.com/i/status/2054632543475896349
Karanta Jadawalin yawan mutanen dake dauke da cutar Kanjamau a kowace jihar Najeriya

Karanta Jadawalin yawan mutanen dake dauke da cutar Kanjamau a kowace jihar Najeriya

Duk Labarai
Wannan jadwalin mutanen dake karbar magungunan cutar Kanjamau ne a kowace jihar Najeriya. 1. Benue: 195,3052. ⁠Akwa Ibom: 158,2013. ⁠Lagos: 135,9184. ⁠Rivers: 90,0555. ⁠Nasarawa: 65,9966. ⁠FCT: 62,6277. ⁠Kaduna: 58,5768. ⁠Cross River: 57,7659. ⁠Enugu: 55,47810. ⁠Delta: 52,47511. ⁠Taraba: 51,84012. ⁠Abia: 50,03813. ⁠Imo: 47,86314. ⁠Plateau: 46,61815. ⁠Anambra: 46,60216. ⁠Adamawa: 42,07417. ⁠Kano: 41,09318. ⁠Kogi: 37,30119. ⁠Oyo: 33,13320. ⁠Niger: 33,05721. ⁠Ogun: 31,82222. ⁠Bauchi: 29,74523. ⁠Edo: 29,25624. ⁠Gombe: 28,03725. ⁠Osun: 25,01826. ⁠Borno: 24,52727. ⁠Ondo: 22,45528. ⁠Kebbi: 20,80329. ⁠Bayelsa: 19,54930. ⁠Katsina: 18,68231. ⁠Ebonyi: 15,47432. ⁠Kwara: 14,99733. ⁠Jigawa: 14,30234. ⁠Zamfara: 13,81335. ⁠Ekiti: 12,35636. ⁠Yobe: 10,71637. ⁠Sokoto: 10,511 Total: 1.70m...
Kalli Bidiyon: Matar tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na rawa da ya dauki hankula

Kalli Bidiyon: Matar tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na rawa da ya dauki hankula

Duk Labarai
Ganin Bidiyon matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari tana rawa ya dauki hankula a kafafen sada zumunta. A'isha Buhari ta yi rawar ne tare da wasu malaman Jinya mata inda suka yi amfani da wani salon wakar da ake yayi na jefa kyalle. Sun yi wannan ne dan murnar zagayowar ranar Malam Jinya ta Duniya https://twitter.com/i/status/2054300515463229822
Kalli Bidiyon da Duminsa: Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu(Me babban Shago) zata yi aure

Kalli Bidiyon da Duminsa: Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu(Me babban Shago) zata yi aure

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu Me babban shago zata yi aure. Hakan ya bayyana ne bayan data wallafa wani Bidiyo inda aka ganta sanye da doguwar riga. A comment an ga wadanda suka santa suna ta tayata murna da fadin Allah ya kaimu ranar auren ita kuma tana ta amin. Saidai Bidiyon ya dauki hankula bayan da aka ga wani sabon zanen Tattoo da Rahama Saidu ta yi a gadon bayanta. https://www.tiktok.com/@rahamasaidu2/video/7638962049204129032?_r=1&_t=ZS-96IkIqZ8a2K A kwanakin baya dai, Rahama Saidu ta dauki hankula bayan da ta yi zanen Tattoo akan kirjinta. Saidai zuwa yanzu ba'a san wanene Rahama Saidun zata aura ba.