
Hirar da ‘yan Jarida suka yi da Shugaba Tinubu ta nuna bai damu da halin da mutane ke ciki ba>>Inji PDP
Jam'iyyar hamayya ta PDP ta bayyana cewa, hirar da 'yan Jarida suka yi da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta farko tun bayan hawansa mulki a Ranar Litinin ta nuna cewa bai damu da halin da 'yan Najeriya ke ciki ba.
Me magana da yawun PDP, Debo Ologunagba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda yace maganar da shugaban kasar yayi ta cewa bai yi nadamar cire tallafin man fetur ba ta nuna bai damu da halin da mutane ke ciki ba.
Yace shugaban kasar kamata yayi ya nuna damuwa akan halin da mutane ke ciki da kuma bayyana hanyoyin da zasu dauka dan kawowa mutane sauki.
Yace ba gaskiya bane maganar shugaban kasar ta cewa an samu ci gaba a kasarnan bayan hawan mulkinsa, inda yace mutuwar da aka rika yi wajan turmutsutsu na karbar abincin tallafi alamace dake nuna irin halin kun...