Friday, May 23
Shadow

Duk Labarai

Najeriya ta fada Duhu yayin da matsalar wutar lantarki ta sake aukuwa, Ji Jihohinnda lamarin ya shafa

Najeriya ta fada Duhu yayin da matsalar wutar lantarki ta sake aukuwa, Ji Jihohinnda lamarin ya shafa

Duk Labarai
'Yan Najeriya sun fada duhu biyo bayan sake samun matsala da wutar lantarkin kasar ta yi. Wannan shine karo na 3 da wutar lantarkin kasar ke samun matsala a shekarar 2024. Da Misalin karfe 1:50 pm. Na ranar Talata ne wutar lantarkin ta sake samun matsala. Kamfanin kula da wutar na kasa,TCN ya tabbatar da hakan amma yace ba gaba daya wutar bace ta samu matsala. Kakakin hukumar, Ndidi Mbah ne ya tabbatar da hakan inda yace injiniyoyinsu na aiki tukuru dan dawo da wutar. Ya kara da cewa An samu dawo da wutar a babban birnin tarayya Abuja kuma suna kokarin dawo da ita a sauran jihohi.
Bayan da ya tsere daga Najeriya, Dan Daudu Bobrisky ya wallafa Bidiyo yana kirga daloli

Bayan da ya tsere daga Najeriya, Dan Daudu Bobrisky ya wallafa Bidiyo yana kirga daloli

Duk Labarai
Shahararren dan daundu, Bobrisky wanda ya sha dambarwar kame daga hukumomin Najeriya amma daga baya ya samu tsallakewa zuwa kasar waje ya sake bayyana. Ya wallafa hotunan Bidiyo yana wasa da dalolin Amirka. https://twitter.com/Chrisvlognation/status/1853869625794302249?t=oy2yERZfQhy_nqkrTmyhlw&s=19 Wani har ya tsokaneshi da cewa aro kudin yayi amma ya mayar masa da martanin cewa a Najeriya ne ake iya yin haka amma banda kasar waje. Bobrisky ya kara da cewa, Wani masoyinsa ne ya bashi wadannan kudade.
Jami’in Hukumar NSCDC ya yanke jiki ya fadi ya mutu jim kadan bayan da aka masa karin girma

Jami’in Hukumar NSCDC ya yanke jiki ya fadi ya mutu jim kadan bayan da aka masa karin girma

Duk Labarai
Jami'in hukumar tsaro ta NSCDC Opatola wanda ba'a dade da karawa mukami ba ya yanke jiki ya fadi ya mutu jim kadan bayan an biyashi Albashi. Yana aiki ne a Iwo kuma ya mutu ne bayan da ya shiga ban daki kamar zai biya bukatarsa. Wasu shaidu sun bayyanawa jaridar The Nation cewa mutumin ya je wajan aiki lafiya kalau a ranar da ya mutu. Abokan aikinsa sun ce sun ga Albashinsu suna korafi akai jim kadan kawai aka ce ai ya mutu.
Mataimakin shugaban kasa Kashin Shettima ya mika matasan da Gwamnati tawa Afuwa zuwa ga Wakilan jihohinsu

Mataimakin shugaban kasa Kashin Shettima ya mika matasan da Gwamnati tawa Afuwa zuwa ga Wakilan jihohinsu

Duk Labarai
Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Sen. Kashim Shettima ya jagoranci bayar da Matasa yan asalin Jihar Kano zuwa ga Wakilan Jihar Kano a Gwamnatin Tarayya wanda suka hada Shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Tarayya, Hon. (Dr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau I Jibril da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf domin dawowa dasu wajen Iyayensu.
Kalli Bidiyo yanda Abba Kabir Yusuf ya sauka daga kujera ya baiwa Kwankwaso ya zauna

Kalli Bidiyo yanda Abba Kabir Yusuf ya sauka daga kujera ya baiwa Kwankwaso ya zauna

Duk Labarai
An ga wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta inda aka ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya baiwa Tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso kujerar da yake zaune dan ya zauna. Hakan na zuwane yayin da rahotanni ke yawo cewa an samu baraka a tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwason. https://www.youtube.com/watch?v=EfYjJ3F6vgM A jiya dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, Jaridar Daily Nigerian tace Abba ya daina daukar wayar Kwankwaso.
Ba zan taba sakin matata ba ko da kuwa na kamata tana cin amanata da wani namiji>>Inji Dan takarar shugaban kasa na Labour party, Peter Obi

Ba zan taba sakin matata ba ko da kuwa na kamata tana cin amanata da wani namiji>>Inji Dan takarar shugaban kasa na Labour party, Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a jami'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa ko da ya kama matarsa tana cin amanarsa da wani namiji ba zai sake ta ba. Peter Obi ya bayyana cewa aminci da soyayyar dake tsakaninsa da matarsa abune me karfi sosai. Peter Obi yace ko da za'a harbeshi da Bindiga ko ya kamata tana cin amanarsa da wani namiji ba zai iya rabuwa da ita ba. Peter Obi yace matarsa idan ta ga dama ta aikata duk abinda take so shidai ba zai iya rabuwa da ita ba. Peter Obi dai da matarsa, Margaret Brownson sun shafe shekaru 30 da aure.