Farfesa Farooq Kperogi ya nemi gafarar Hajiya A'isha Buhari, inda ya røƙeta da ta yi masa afuwa bisa kuskurēɲ da ya aikata.
Ya ce ya yaɗa labarin ƙarya a shafinsa na Fäcebøøk cewa Buhari ya saki A'isha kafin rasuwarsa. A cewarsa, yanzu ya gane kuskuren da ya yi kuma yana mai nadama da roƙon afuwa.
Me zaku ce?
Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi Ya Jagoranci Tawagar Kungiyar Mu'assasa Domin Yiwa Gwamna Raɗɗa Ta'aziyyar Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari.
Tawaga ta musamman daga gidauniyar Shehun Malamin nan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi, sun ziyarci Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, domin yi mashi ta'aziyyar rasuwar Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin ɗan Shehin Malamin Ɗariƙar Tijjaniyya Khalifa Ibrahim Ɗahiru Bauchi sun ziyarci Gwamnan ne a gidan gwamnatin jihar Katsina a yau Lahadi 20 ga watan Yuli 2025.
Da yake gabatar da jawabin dalilin ziyarar ta su Khalifa Ibrahim Ɗahiru Bauchi, ya bayyana sun zo ne a madadin mahaifin nasu domin yiwa iyalai, Gwamnan, da kuma a al'ummar jihar Katsina t...
Manajan Otal a kasar Ingila ya kirawa Gwamnan Najeriya da yaje otal din ya kama daki yake watsi da kudi 'yansanda inda yayi tunanin ya haukacene.
Gwamnan ya je otal dinne dan yayi bikin zagayowar ranar Haihuwarsa.
Inda ya rika watsi da takardin Fan 50 da fan 10.
Da 'yansandan suka je otal din, saida abokan gwamnan wanda suma gwamnoni 2 ne da suka ke tayashi murna auka shiga tsakani inda suka cewa 'Yansandan ba mahaukaci bane.
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta bayyana cewa, suna binciken gwamnoni masu ci dake kan kujerunsu a halin yanzu haka guda 18.
Shugaban EFCC din, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a Legas ranar Juma'a data gabata.
Yace a yanzu suna kan binciken gwamnonin ne amma idan suka sauka daga mukaman su na gwamnoni za'a shiga mataki na gaba a binciken.
Reshen Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ya yi watsi da matakin gwamnatin tarayya na sauya sunan jami’ar zuwa sunan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Kungiyar ta soki wannan mataki tana mai cewa “yana da ɗauke da manufar siyasa” kuma “ cin mutunci ne ga tarihin jami’ar da aka kafa tun shekaru.”
Jaridar Leadership ta rawaito cewa shugaban ASUU, reshen UNIMAID, Dr. Abubakar Mshelia Saidu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri wacce jaridar Leadership ta samu a ranar Lahadi, ya bayyana adawa ga wannan mataki.
Kungiyar ta bayyana cewa sauya sunan raini ne ga tarihin UNIMAID mai ɗimbin daraja kuma yana lalata mutuncin kimiyya da jami’ar ta gina tsawon shekaru.
“Wannan mataki abin mamaki ne ƙwarai kuma yana ɓata tsarkin makarantar mu,” in ji ...
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai ci zaben shekarar 2027 ba.
El-Rufai ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a tasher Arise TV inda yace idan Tinubu ya zo na 3 to ya godewa Allah.
El-Rufai yace yayi iya lissafinsa bai ga ta yanda za'a yi Tinubu ya ci zaben shekarar 2027 ba.
'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu Ɗahiru Binani, ta yanki katin jam'iyyar haɗaka ta African Democratic Congress (ADC).
An ga tsohowar 'yarmajalisar dattawan da ta wakilci mazaɓar Adamawa ta Tsakiya cikin wani bidiyo tana jawabin nuna goyon baya ga ADC, yayin da take zagaye da matasa.
"Mu mun ɗauki jam'iyyar ADC kuma za mu yi tafiya a cikinta," in ji ta. "Muna roƙon Allah ya taimake mu ya raba mu da mutanen da muke tafiya da su amma suna gurɓata jam'iyya."
Bayan kammala jawabin ne kuma aka gan ta ɗauke da katin jam'iyyar cikin wasu hotuna.
Binani ta yi takara ne a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, inda ta gwada wa Gwamna Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP zazzafan ƙalubale a zaɓen na 2023.
'Yarmajalisar Dattawan Najeriya Sanata Natasha Akpoti ta ci alwashin komawa majalisar ranar Talata mai zuwa duk da dakatarwar da aka yi mata.
Sanatar mai wakiltar mazaɓar jihar Kogi ta Tsakiya ta ce za ta yi hakan bisa hukuncin kotu, wadda ta ce dakatarwar wata sida da majalisar ta yi mata ta saɓa dokar tsarin mulkin Najeriya.
Sai dai majalisar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, wanda ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisa Godswill Akpabio da ɓata suna.
Da take magana da manema labarai a ranar Asabar, Natasha ta ce ba ta dakatar da aiki ba duk da ba ta zuwa zauren majalisar.
"Zan je [majalisar] da yardar Allah a ranar Talata, saboda kotu ta bayar da hukunci kan hakan. Amma suna cewa wai ai matsaya ce kotun ta ɗauka ba umarni ta bayar ba. Amma tsarin mulk...
Iyalin marigayi Muhammadu Buhari sun bayyana godiya da jin daɗinsu ga gwamnati da 'yan Najeriya bisa karramawar da suka ce an yi wa tsohon shugaban ƙasar na Najeriya bayan rasuwarsa.
A ranar Talata ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jagoranci binne Buhari a gidansa da ke garin Daura na jihar Katsina bayan ya rasu ranar Lahadi a birnin Landan sakamakon doguwar jinya.
Wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun iyalin, ya wallafa yau Lahadi ta ce Mamman Daura ne ya wakilci iyalin wajen miƙa godiyar tasu.
"Mun yi farin ciki da irin kulawar da shugaba ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da ministoci suka ba mu yayin jana'iza a nan Daura," in ji Mamman Daura.
"Muna matuƙar godiya ga shugaban ƙasa da ya ayyana ranar hutu da kuma sanya wa Jami'ar Maiduguri sunan Buhari. Muna kuma amfan...