Saturday, May 24
Shadow

Duk Labarai

Hotuna: Kalli Yanda mata ke neman maza suna biyansu suna lalata dasu

Hotuna: Kalli Yanda mata ke neman maza suna biyansu suna lalata dasu

Duk Labarai
Matan Turawa na zuwa yawon shakatawa a kasar Turkiyya inda suke biyan matasan kasar suna lalata dasu. Garin dai gabar teku yake inda ake kiransa da sunan Marmaris. Matan turawan dake tsakanin shekaru 20 zuwa 70 na tururuwa sosai zuwa wannan gari dan neman matasan kasar na Turkiyya su biya musu bukatunsu. Katie me shekaru 22 wadda taje wannan gabar tekun ta kasar Turkiyya daga yankin Wales na kasar Ingila ta bayyana cewa tana da saurayi Omar dake biya mata bukatarta kuma ya iya kwanciya da mace. Tace duk da tasan yana da wasu mata 10 da yake kwanciya dasu amma hakan bai dameta ba dan kuwa tazo jin dadine kawai. Jaridar theSun ta kasar Ingila ta ruwaito cewa akwai wani Facebook group da aka bude ake tozarta mata da maza dake irin wannan aikin masha'a a kasar ta Turkiyya wanda...
‘Yan Bindiga sun kashe ‘yansanda 5 da sojoji 2 a Jihar Zamfara

‘Yan Bindiga sun kashe ‘yansanda 5 da sojoji 2 a Jihar Zamfara

Duk Labarai
Kwamishinan 'yansandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalinja ya tabbatar da mutuwar 'yansanda 5 da sojoji 2 wanda 'yan Bindiga suka kashe a karamar hukumar Tsafe dake jihar. Ya bayyana cewa 'yan Bindigar sun yiwa jami'an tsaron kwantan baunane inda suka bude musu wuta a kan hanyar Gusau zuwa Funtua ranar Alhamis. Ya bayyana cewa, 'yan Bindigar sun tafi kaiwa kamfanin gini na Setraco Company Hari ne inda jami'an tsaron suka samu bayanan sirri suka tafi dan taresu. Yace yanda aka yi suka kashe musu jami'ai kenan.
‘Yan kasuwar Man fetur da yawa basa sayen man fetur din daga matatar mu>>Dangote

‘Yan kasuwar Man fetur da yawa basa sayen man fetur din daga matatar mu>>Dangote

Duk Labarai
Wakilin kamfanin Dangote, Devakumar V. G. Edwin ya bayyana cewa, mafi yawan 'yan kasuwar man fetur na Najeriya basa sayen man fetur din daga matatarsu. Ya bayyana hakane a wata hira ta musamman da aka yi dashi inda yace kaso 95 na 'yan kasuwar man fetur din basa saye daga wajensu. Yace hakan yasa dole suke fitar da man fetur din nasu zuwa wasu kasashe dan sayarwa.

Gwamnoni sun kai ziyarar jaje zuwa Maiduguri

Duk Labarai
Gwamnonin wasu jihohin Najeriya sun ziyarci birnin Maiduguri domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa iftila'in ambaliya da ya auka wa birnin. Gwamnonin da suka ziyarci Maidugurin sun haɗa da na Legas Babajide Sanwo Olu da na Ondo, Lucky Aiyedatiwa da na Adamawa, Umar Fintiri da kuma na Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq. Gwmanan Legas - wanda ya bayyana ambaliyar a matsayin mummuna - ya ce gwamnonin sun jajanta wa iyalan mutanen da lamarin ya shafa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X. ''A matsayinmu na al'umma ɗaya yana da muhimmanci mu haɗa kai don samar da agaji da taimaka wa aikin ceto, tare da tabbatar da cewa waɗanda lamarin ya shafa sun samu tallafin da suke buƙata'', in ji Gwamnan Sanwo Olu.
Gwamnan Zamfara ya ɗauki nauyin karatun zaƙaƙuran ɗaliban jihar

Gwamnan Zamfara ya ɗauki nauyin karatun zaƙaƙuran ɗaliban jihar

Duk Labarai
Gwamnan jihar Zamfara a arewacin Najeriya ya ba wa wasu zaƙaƙuran dalibai 30 tallafin karatu domin su yi karatu a sakandiren gwamnatin tarayya ta Federal Government Academy da ke Suleja ta jihar Neja. Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da yake ganawa da ɗaliban da kuma jagorancin Cibiyar Muhammad Kabir Danbaba Centre for Women and Youth Development Center a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau. Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce cibiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da jihar ta Zamfara ke samu a ɓangaren ilimi. Sanarwar ta ƙara da cewa yawancin ɗaliban da suka fi samun nasara na makarantun gwamnati ne. "Wannan nasarar da kuka samu ta nuna cewa gwamnatinmu na ƙoƙari wajen inganta ilimi," a cewar Gwamna Dauda Lawal.
Shugaba Tinubu ya gana da Sarki Charles na Ingila

Shugaba Tinubu ya gana da Sarki Charles na Ingila

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana Sarki Charles na Ingila a fadarsa ta Buckingham da ke birnin Landan. Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana ganawar a matsayin ta sirri, wadda ta ƙara nuna alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya. "Shugabannin sun tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashensu, musamman matsalar sauyin yanayi," kamar yadda sanarwar ta bayyana. Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu da Sarki Charles sun tattauna hanyoyin da za su iya yin haɗaka musamman a daidai lokacin da ake shirin taron COP 29 da ke tafe a ƙasar Azerbaijan da kuma taron ƙasashe rainon Ingila wato CHOGM da za a yi a Samoa. Ya ce: "Tinubu ya ƙara nanata ƙudurin Najeriya na...
Tinubu ya bai wa jihohi naira biliyan 108bn kan ambaliya da zaizayar ƙasa – Shettima

Tinubu ya bai wa jihohi naira biliyan 108bn kan ambaliya da zaizayar ƙasa – Shettima

Duk Labarai
Tinubu ya bai wa jihohi naira biliyan 108bn kan ambaliya da zaizayar ƙasa - Shettima. Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da kuɗi Naira biliyan 108 ga jihohi 36 na ƙasar domin yaƙi da ambaliya da sauran nau'ukan bala'o'i. Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba. Da yake bayyani a lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Abbas Tajudden, ya bayyana ambaliyar ta Borno a matsayin "bala'i ga ƙasar baki ɗaya." "Shugaba ƙasar ya nuna niyyarsa ta haɗa hannu da jihohi domin magance irin waɗannan matsalolin," inji Shettima. "Ba a daɗe ba ya amince a ba kowace jiha Naira biliyan uku domin magance irin waɗannan matsalolin," kamar yadda shafin talabijin na Ch...