Idan ADC na son kayar da Tinubu a 2027 sai Atiku ya rage son rai ya zama mataimakin Peter Obi>>Inji Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohaneze Indigbo
Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayar da shawarar cewa, Muddin Jam'iyyar ADC na son kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 sai Atiku ya rage son rai ya zama mataimakin Peter Obi.
Kungiyar ta bayyana hakane a ranar Litinin a wata sanarwa da shugaban matasa na Kungiyar, Igboayaka O. Igboayaka ya fitar.
Yace Peter Obi na da dukkan abinda ake bukata da zasu kai kasarnan ga ci gaba.








