Sunday, January 12
Shadow

Duk Labarai

Sowore ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar su je su shiga gidaje 753 na Abuja da gwamnati ta kwace saboda nasu ne

Sowore ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar su je su shiga gidaje 753 na Abuja da gwamnati ta kwace saboda nasu ne

Duk Labarai
Mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya baiwa 'yan Najeriya shawarar su je su kammala ginin rukunin gidaje 753 da gwamnati ta kwace a Abuja su ci gaba da zama a ciki saboda gidajen nasu ne. Ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter. https://twitter.com/YeleSowore/status/1863671862175166904?t=WysOD6GSPJtaBSMTjA6nFg&s=19 Gidajen dai a cewar hukumar EFCC sune kadara mafi girma da suka taba kwacewa tun bayan kafa hukumar. Bayanan kotu sun nuna cewa, an kwace gidajenne daga hannun tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele saidai EFCC taking ambatar sunan tsohon gwamnan CBN din inda tace an kwace kadarorinne daga hannun wani tsohon jami'in gwamnati.
ALHAMDULILLAH: Sheik Maqari Ya Zama Mutum Na Farko Da Ya Fi Kowa Ilmin Hadisi A Fadin Afrika

ALHAMDULILLAH: Sheik Maqari Ya Zama Mutum Na Farko Da Ya Fi Kowa Ilmin Hadisi A Fadin Afrika

Duk Labarai
An zaɓi Farfesa Maqari daga Nijeriya a matsayin wanda ya fi kowa ilimin sanin Hadisan Manzan Allah SAW a kaf Nahiyar Afrika. Babbar Jami'ar Musulunci ta farko wacce aka fi sani da Jami'atul Al'azahar dake ƙasar Masar ce ta ayyana babban limamin masallacin kasa Fafesa Maqari a matsayin wanda ya fi kowa ilimin sanin Hadisan Annabi da na Fiqhu. Wace fata kuke masa? Daga Abba Abdulaziz Fari Funtua
Ina goyon bayan kudirin dokar canja fasalin karba da raba Haraji a Najeriya>>Inji Bishop Kukah

Ina goyon bayan kudirin dokar canja fasalin karba da raba Haraji a Najeriya>>Inji Bishop Kukah

Duk Labarai
Bishop Kukah Wanda babban malamin Kiristane ya bayyana goyon bayansa da amincewa da kudirin dokar canja yanda ake karba da raba Haraji a Najeriya. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Kuka yace sabuwar dokar zata bayar da damar kawo canji kan yanda ake kashe kudi ba kai ba gindi. Yace kuma dokar zata karfafa gasa tsakanin jihohi ta hanyar samun kudin shiga.
Gaddama ta kaure tsakanin Sowore da EFCC inda ya zargesu da yin rufa-rufa akan maganar kwace gidaje 753

Gaddama ta kaure tsakanin Sowore da EFCC inda ya zargesu da yin rufa-rufa akan maganar kwace gidaje 753

Duk Labarai
Maganar kwace gidaje 753 daga hannun tsohon gwamnan babban banking Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ta jawo cece-kuce tsakanin hukumar EFCC da mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore. EFCC a yayin da ta wallafa maganar kwace gidajen tace an kwacesune kawai daga hannun wani babban jami'in Gwamnati ba tare da fadar sunanshi ba. Dalilin hakane Sowore ya zargi EFCC da yin rufa-rufa akan lamarin inda yace daga hannun Emefiele ne aka kwace gidajen. Saidai EFCC ta musanta hakan, a martaninsa, Sowore ya wallafa takardun kotun Wanda suka nuna yanda aka zartar da hukuncin kwace gidajen da sunayen mutanen sake da hannu a lamarin.
An gano cewa, Tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele ne ya mallaki gidaje 753 da gwamnati ta kwace

An gano cewa, Tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele ne ya mallaki gidaje 753 da gwamnati ta kwace

Duk Labarai
A jiyane muka samu labarin cewa, kotu a Abuja ta kwace wasu gidaje 753 daga hannun wani tsohon ma'aikacin gwamnati inda ta mallakawa gwamnatin tarayya su. Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ce ta bayyana haka a wata sanarwa data fitar inda tace kamen shine mafi girma da aka taba yi a tarihinta. Saidai bata bayyana sunan jami'in gwamnatin data kwace wadannan kadarorin daga hannunsa ba. A sabon rahoton da muka samu, Mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ne aka kwace wadannan gidaje daga hannunsa. Emefiele dai tun hawan mulkin shugaba, Bola Ahmad Tinubu ake bincikensa da laifuka daban-daban.
Hotuna: EFCC ta yi babban kamun da bata taba yin irinsa ba

Hotuna: EFCC ta yi babban kamun da bata taba yin irinsa ba

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC ta yi babban kamun da bata taba yin irinsa ba run bayan kafata a shekarar 2003. Hukumar CE ta sanar da haka a shafinta na sada zumunta. Tace kotu ta kwace wasu gidaje 753 da aka Gina da kudin sata. Saidai EFCC bata bayyana sunan Wanda ta kwace kadarorin daga hannunsa ba, Inda kawai race babban jami'in gwamnatine. Tace taba ci gaba da bincikensa.