Tauraruwar Tiktok Rahama Saidu ta bayyana cewa, ta daina shigar banza.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyo da aka ganta tare da rashida mai sa'a inda take mata nasiha akan Saka Hijabi.
Kalli Bidiyon nan:
https://www.instagram.com/reel/DNh2awNKsDR/?igsh=MXJobDV2anJ5bGd5YQ==
Hukumar hana yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa, EFFC ta bayyana cewa, zata fara binciken tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari kan zargin satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man Najeriya.
Hakan na zuwane bayan da tuni kotu ta kulle asusun ajiyarsa na banki guda 4 dake dauke da makudan kudade.
Rahoton Daily Trust yace tuni aka fara binciken wasu na kusa da Kyari inda EFCC tace tana son samun isassun bayanai akanshi kamin ta fara bincikenshi.
Game da cewa, Kyari baya Najeriya, Hukumar tace wannan ba matsala bane da zarar sun bukaci kamashi ko bincikenshi kamashi ba abune me wuya ba.
Dan majalisar wakilai na majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude ya nada masu taimaka masa guda 106.
Ya bayyana hakane a hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace ya nada mutane 106 a matsayin masu taimaka masa ne dan ya tallafawa rayuwarsu.
Yace daga ciki akwai wadanda yake biya albashin Naira Dubu 10 har zuwa Dubu 100.
Dan majalisar wanda a jam'iyyar SDP yake daga mazabar Uke/Karshi yace ya tallafawa mutane a bangarori daban-daban da suka hada da Noma, ilimi, da sauransu.
Tauraruwar fina-finan Hausa Mansurah Isah tace an nadata mukamin Jakadiyar Fim ta zama Lafiya ta Hausawan Duniya.
Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace mahaifiyar ta, Hajiya Maijidda Ado Bayero kuma an nadata mukamin Sarauniyar Hausa da Hausawan Duniya.
Yadda Wani Bawan Allah Ya Zube Ruwan Leda (Pure Water) A Gefen Titin Area 11 Dake Abuja Saboda Masu Bukata
Wace fata za ku yi masa?
Saidai abin tambaya shine, za ka iya dauka ka yi amfani da shi idan bukatarsa ta taso maka duk da cewa ba ka san wa ya ajiye ba?
Mata a birnin Legas sun yi barazanar yin zanga-zangar tsirara dan tursasa daina rushe musu gidaje.
Matan daga yankin Ilaje sun yi zanga-zangar lumana zuwa majalisar dokokin jihar ta Legas inda suka nemi taimakon gwamnan jihar, Babajide Sonwo Olu da kakakin majalisar Dokokin jihar,Mudashiru Obasa su saka baki a daina rushe musu gidaje.
Sun zargi sarakunan gargajiyarsu da yi musu kwacen gidaje.
Daya daga cikin matan wadda dattijuwa ce, ta fito inda take barazanar cewa, zasu yi zanga-zanga tsirara idan ba a daina rushe musu gidaje ba.
Shima shugaban mazauna yankin na Ilaje, Rafael Irowainu ya bayyana cewa wasu sarakuna na amfani da sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna rushe gidaje dan su yi gine-gine.
Ya kara da cewa, amma basu yadda shugaba ne ya aika mutanen ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa Wajan taro a Birnin Tokyo na kasar Japan inda yake halartar taro na musamman da ake gudanarwa kan ci gaban Afrika.
https://twitter.com/DOlusegun/status/1958044993508999348?t=dEN0LgE5LuBR0cmMo12VHw&s=19
Gwamnan riko na jihar Katsina wanda gwamna Dikko Radda ya barwa jihar a hannunsa Malam Faruk Lawal-Jobe ya yi kira ga gwamnatin tarayya data kawo musu dauki a jihar game da tabarbarewar lamuran tsaro.
Wannan kira nasa na zuwane bayan harin da 'yan Bindiga suka kai unguwar Muntau dake garin Malunfashi a jihar Katsina suka kashe mutane akalla 13 dake sallar Asuba.
Hakanan maharan sun rika harbin kan mai uwa da wabi inda kuma suka sace mutane 60, kamar yanda kafar Rariya ta tuwaito.
Hakan na zuwane a yayin da Gwamna Dikko Radda ke kasashen Turawa nema Lafiya amma an hangoshi a wasu hotuna yana daukar hoton garin da yaje.
Gwamnan rikon, Malam Faruk Lawal-Jobe ya nemi gwamnatin tarayya data kawowa jihar dauki lura da yanda lamuran tsaro suka tabarbare tare da neman Shugaban kasa ya ...
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya soke karin kaso 5 akan kamfanonin Sadarwa da ake shirin yi.
Shugaban hukumar NCC, Aminu Maida ne ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai.
Yace karin harajin kaso 5 akan kamfanonin sadarwar yana kunshene a cikin sabon kudirin dokar da majalisa ta amince dashi.
Yace yana wajan aka kawowa shugaba Tinubu maganar karin amma yace ba zai kara saka 'yan Najeriya a cikin matsala ba.
Yace a baya an dakatar da karinne amma yanzu an cireshi gaba daya.