Ji dalilin da ya sa yawanci shugabannin jam’iyyu a Najeriya ke sauka ba girma ba arziki?
A ranar Juma'a ne shugaban jam'yyara APC na Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya a jiye muƙaminsa na jangorancin jam'iyyar.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya sauka da muƙamin nasa ne bayan shafe kusan shekara biyu riƙe da shugabancin jam'iyyar a matsayin riƙo bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan.
"Da gaske ne Ganduje ya sauka tun ranar Alhamis aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a ranar Juma'a da safe miƙa takardar," in ji majiyar.
Kusan a iya cewa ya zama al'ada a tsarin siyasar Najeriya kusan duka mutanen da suka jagoranci manyan jam'iyyun ƙasar ba sa wanyewa lafiya da muƙaman nasu.
Wasu daga cikinsu ana dakatar da su...








