Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

Sanata Neda Imasuen ya bar jam’iyyar Labour party zuwa APC

Sanata Neda Imasuen ya bar jam’iyyar Labour party zuwa APC

Duk Labarai
Sanata Neda Imasuen daga jihar Edo ya bar jam'iyyar Labour Party inda ya koma jam'iyyar APC inda yace rikicin cikin gida ya mamaye jam'iyyar ta APC. Ya bayyana ficewarsa daga Labour party zuwa APC a zaman majalisar Dattijai na ranar Laraba. Kakakin majalisar, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan inda ya karanto takardar da sanata Nedu ya aikawa majalisar. Yace kamin yanke wannan shawara sai da ya tuntubi da yawa daga cikin abokan shawararsa da mutanen mazabarsa da sauransu.
Duk malamin cocin da ya kai mukamin Priest dole ne ya hakura da jìma’ì saboda tsoron Allah>>Fafaroma ya jaddada dokar cocin Katolika

Duk malamin cocin da ya kai mukamin Priest dole ne ya hakura da jìma’ì saboda tsoron Allah>>Fafaroma ya jaddada dokar cocin Katolika

Duk Labarai
Fafaroma Leo XVI ya jaddada cewa dolene duk wanda ya kai mukamin Priest ya hakura da yin jima'i a rayuwarsa saboda tsoron Allah. Ya bayyana hakane a ranar Laraba inda yace Bishops su tashi tsaye dan hukunta masu karya wannan doka da kuma cin zarafin mata da yara. Yayi bayanin ne ga Bishops guda 400 da suka fito daga kasashe 38 na Duniya. A lokuta da dama dai ana samun jagororin cocin suna lalata da yara ko cin zarafin matan dake halartar cocinsu.
Kalli Bidiyo: Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a harin Jihar Benue

Kalli Bidiyo: Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a harin Jihar Benue

Duk Labarai
Sufeto Janar na ‘ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi a al’ummar Yelwata da ke ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benue, ranar 13 ga Yuni, 2025. Egbetokun ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 47 a cikin harin, yayin da wasu 27 kuma suka jikkata kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. Rundunar ‘yan sanda ta ce an kuma kashe wasu biyu daga cikin ‘yan harin a ranar da lamarin ya faru. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1937832392464441518?t=girIfCT6i0I0_OrwQt0kgA&s=19 Egbetokun ya ce an tura jami’an tsaro domin bin diddigin lamarin, kuma daga baya an kama wasu manyan masu hannu biyu-biyu a kisan wanda hakan ya kai ga kama karin mutum bakwai.
Me sayar da motoci ya koka bayan da wani ya sayi Motar Naira Miliyan 45 kuma ya biya kudin tun shekarar 2023 amma bai je ya dauki motar tasa ba

Me sayar da motoci ya koka bayan da wani ya sayi Motar Naira Miliyan 45 kuma ya biya kudin tun shekarar 2023 amma bai je ya dauki motar tasa ba

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani me sayar da motoci ya koka saboda wani ya sayi motar Naira Miliyan 45 a hannunshi kuma ya biya kudin tun shekarar 2023 amma bai je ya karbi motarba. da yawa aun jinjinawa me sayar da motocin inda suka ce ba kowane zai iya abinda yayi ba.
Shugaba Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi

Shugaba Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kafa rundunar tsaro ta musamman a garin Zuru na jihar Kebbi. Gwamnan jihar, Nasir Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai kauyukan karamar hukumar Danko da Wasagu inda 'yan Bindiga suka kashe mutane 30. Yace za'a kafa rundunar tsaronne dan inganta tsaro a jihar dama yankin baki daya. Gwamnan yace yanzu haka ya yi kokarin an kai jami'an tsaro da makamai inda lamarin ya faru.
Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan adam na DSTV ya rage farashi daga dubu 20 zuwa dubu 10 bayan da ya tafka asarar kudade saboda mutane sun daina kallo

Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan adam na DSTV ya rage farashi daga dubu 20 zuwa dubu 10 bayan da ya tafka asarar kudade saboda mutane sun daina kallo

Duk Labarai
Kamfanin Multichoice dake da tauraron dan Adam na DSTV sun sanar da rage farashin da ake biya dan kallo duk wata daga Naira dubu 20 zuwa Naira Dubu 10. Hakan na zuwane bayan da kamfanin ya tafka asarar miliyoyin kudade saboda da yawan 'yan Najeriya sun daina saka kudi dan kallon. Saidai abin jira a gani shine ko hakan zai sa mutane a yanzu su dawo su ci gaba da biyan kudi dan kallon DSTV din?
Kalli Bidiyon yanda Amarya, Maryam Malika ta fashe da kuka a wajen bikinta

Kalli Bidiyon yanda Amarya, Maryam Malika ta fashe da kuka a wajen bikinta

Duk Labarai
Amaryar Abdul M. Shareef watau Maryam Malika wadanda dukansu 'yan fim ne ta fashe da kuka a wajan bikinta. A cikin wani Bidiyon ta da aka ga yana yawo a kafafen sada zumunta, An ga Malika na zubar da hawaye inda kawayenta da yawa ke bata baki. https://www.tiktok.com/@amb_musty/video/7519650466523827512?_t=ZM-8xUm2pm19rc&_r=1 Saidai wasu sun yi mamakin ganin kukan Malika a ranar aurenta, musamman ma ganin cewa bazawara ce.
Garama ka hakura, Ba zaka kai labari ba a zaben 2027>>Wani jigo a jam’iyyar APC ya baiwa Tinubu shawara

Garama ka hakura, Ba zaka kai labari ba a zaben 2027>>Wani jigo a jam’iyyar APC ya baiwa Tinubu shawara

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani jigo a jam'iyyar APC ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar kada ya nemi sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027. Eze Chukwuemeka Eze daga jihar Rivers ya yabawa El-Rufai da Amaechi da Atiku da sauransu da suka hada kai dan kafa sabuwar jam'iyya me suna ADA dan su kayar da Tinubu a zaben shekarar 2027. Yace Tinubu bai yiwa 'yan Najeriya wani aikin a zo a gani ba a shekaru 2 da yayi yana mulkar Najeriya inda yace dan haka ya kamata ya hakura kar y...
Jihar Kebbi na son saka dokar kisa ga masu baiwa masu garkuwa da mutane bayanan sirri

Jihar Kebbi na son saka dokar kisa ga masu baiwa masu garkuwa da mutane bayanan sirri

Duk Labarai
Jihar Kebbi na son saka dokar kisa ga masu baiwa masu garkuwa da mutane bayanan sirri. Gwamnan jihar, Comrade Nasiru Idris yace zasu saka dokar kisa ko kuma daurin rai da rai ga masu baiwa masu garkuwa da mutanen bayanan sirri. Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara kauyukan Tadurga da Zuru da Kyebu inda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda 'yan Bindiga suka kashe. Kauyukan na kananan hukumomin Danko/Wasagu dake jihar kuma kwanannan aka kai hare-hare wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 30 da kuma sace shanu da yawa. Gwamnan ya bayyana cewa, zasu dauki matsalar tsaro da matukar muhimmanci a jihar.