Dalori ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaban APC na riƙo
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa, Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na riƙo.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan na jihar Kano ya ajiye muƙamin a ranar Juma'a, sannan aka naɗa Dokta Ali Bukar Dalori a matsayin wanda zai riƙe muƙamin, kafin a kai ga zaɓen wanda zai maye gurbinsa.
Mutane dai sun yi zargin ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya amma uwar jam'iyyar ta yi watsi da wannan hasashe.
Bala Ibrahim shi ne daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar ta APC, ya ce "Game da batun wanda zai maye gurbin shugaban jam'iyyar da sauka, dama jam'iyya na da kundin tsarin mulki wanda ya yi tanadi irin wannan wanda idan shugaban jam'iyya ya sauka daga muƙaminsa to za a zaɓi ɗaya daga cikin mataimakansa biyu...








