Wednesday, March 4
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Na tuba nawa Mijina Alkawarin ba zan sake yin abin zubar da mutunci ba a kafafen sada zumunta>>Sadiya Haruna

Kalli Bidiyo: Na tuba nawa Mijina Alkawarin ba zan sake yin abin zubar da mutunci ba a kafafen sada zumunta>>Sadiya Haruna

Duk Labarai
Tauraruwar kafafen sada zumunta, Sadiya Haruna ta bayyana cewa tawa Allah, da iyayenta, da mijinta, da Abokan arziki alkawarin ba zata sake yin abin zubar da Mutunci ba a Tiktok. Sadiya ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa inda take martani kan wasu dake amfani sa sunanta suna damfarar mutane. Sadiya ta jawo hankalin masu yin da cewa su daina. https://www.tiktok.com/@sayyada_sadiya_haruna/video/7536109780876774662?_t=ZS-8ykjnvbeoV7&_r=1
Nasarorin Shekaru biyun Tinubu ta wuce ta mulkin Obasanjo kawo ayyukan ci gaba – Fadar Shugaban Ƙasa

Nasarorin Shekaru biyun Tinubu ta wuce ta mulkin Obasanjo kawo ayyukan ci gaba – Fadar Shugaban Ƙasa

Duk Labarai
Nasarorin Shekaru biyun Tinubu ta wuce ta mulkin Obasanjo kawo ayyukan ci gaba - Fadar Shugaban Ƙasa Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya cimma wa a shekarun sa guda biyu na mulki, ya wuce wanda PDP ta yi a ƙarƙashin Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007. Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwa Daniel Bwala ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya fitar a shafin sa na X a ranar Juma'a. Ya ce PDP a ƙarƙashin Obasanja ta samu tagomashi daga duniya ciki har da yafe mata bashi da samun gangar mai da yawa da fata na ƙasashe bayan dawowa mulkin dimokuraɗiyya. Daga Usman Salisu
Kalli Bidiyon tallar A sake zaben shugaba Tinubu a 2027 da taurarin Kannywood ke yi ya jawo cece-kuce sosai

Kalli Bidiyon tallar A sake zaben shugaba Tinubu a 2027 da taurarin Kannywood ke yi ya jawo cece-kuce sosai

Duk Labarai
An ga Bidiyon yanda taurarin fina-finan Hausa na Kannywood suke tallar a sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027. A Bidiyon an ga irin su Rahama Sadau, Ali Nuhu, Ado Gwanja, Aminu Sharif Momo, Sadiq Sani Sadiq da sauransu suna tallar a sake zaben shugaban kasar. https://www.tiktok.com/@zafafa.kannywood/video/7535786141665103110?_t=ZS-8yk9LGW5KwS&_r=1 Da yawa dai sun nuna rashin jin dadin ganin wannan tallar.
Dan Sarkin Kano, Adam Muhammad Sanusi ya ce mutane su daina zargin babansa kan wahalar da suke ciki da maganar cire tallafin man fetur inda wasu ke ganin kamar baban nasa ne ya zuga aka cire tallafin

Dan Sarkin Kano, Adam Muhammad Sanusi ya ce mutane su daina zargin babansa kan wahalar da suke ciki da maganar cire tallafin man fetur inda wasu ke ganin kamar baban nasa ne ya zuga aka cire tallafin

Duk Labarai
Dan gidan sarkin Kano, Adam Lamido Sanusi ya jawo hankalin masu sukar mahaifinsa game da cewa shine ya zuga aka cire tallafin man fetur dan haka ake zarginsa da wahalar da ake ciki. Yace ba gaskiya bane, babansa bai bayar da shawarar cewa a cire tallafin man fetur a lokaci guda ba. Yace da an cire tallafin man fetur din tun a lokacin da mahaifiyarsu ya bayar da shawarar a cire tallafin da ba'a shiga wahalar da ake ciki ba. Ya kara da cewa, Biyan Tallafin man fetur ya lakume kudin Najeriya gaba daya ta yanda sai an rika ciwo bashi ake iya biyan tallafin. Yace kuma mutane na karya su ce sun shigo da man fetur daga kasashen waje dan a basu tallafin. Yace kuma ana daukar man fetur dun na Najeriya da aka biya tallafi akansa akai shi kasashe makwabta a rika sayarwa da tsada. ...
Kalli Bidiyon farko da Rahama Sadau ta saki bayan bayan daura aurenta da sauran Bidiyon da baku gani ba na bikin

Kalli Bidiyon farko da Rahama Sadau ta saki bayan bayan daura aurenta da sauran Bidiyon da baku gani ba na bikin

Duk Labarai
Bayan daura aurenta, Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta wallafa Bidiyo inda ta tabbatar da cewa lallai ta yi aure. Kalli Bidiyon anan https://www.tiktok.com/@ayeesha_sadau/video/7536535160301341957?_t=ZS-8yjs1I8RTn7&_r=1 https://www.tiktok.com/@ayeesha_sadau/video/7536566464183127352?_t=ZS-8yjs4TFj7rd&_r=1 https://www.tiktok.com/@ayeesha_sadau/video/7536629172135906616?_t=ZS-8yjs7dMq8cD&_r=1
Idan ADC ta tsayar dani takara babu shakka zan kayar da Shugaba Tinubu zabe a 2027>>Rotimi Amaechi

Idan ADC ta tsayar dani takara babu shakka zan kayar da Shugaba Tinubu zabe a 2027>>Rotimi Amaechi

Duk Labarai
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, idan jam'iyyar ADC ta bashi takarar shugaban kasa a zaben 2027 tabbas zai kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Ya bayyana hakane a kafarsa ta X. Zan canja kundin tsarin mulki, zan kawo ƙarshen cin hanci cikin wata idan na zama shugaban ƙasa - Amaechi Tsohon Ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya jaddada cewa zai canja kundin tsarin mulkin Najeriya idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2027. Amaechi ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a shafin sa na X a ranar Juma'a, inda yace zai kawo karshen matsalar cin hanci a cikin wata daya ko ya sauka daga mulki. Amaechi ya kuma bayyana Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin lalataccen shugaban hukumar zaɓe a tarihin Najeriya. Daga Usman Salisu
Kalli Bidiyo: Allah ya tsynewa me karya, Sheikh Salihu Zaria ya gayawa Ministan tsaro, Muhammad Badaru kan ikirarin da ministan yayi cewa an sami tsaro a Arewa

Kalli Bidiyo: Allah ya tsynewa me karya, Sheikh Salihu Zaria ya gayawa Ministan tsaro, Muhammad Badaru kan ikirarin da ministan yayi cewa an sami tsaro a Arewa

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya bayyana cewa, Allah ya tsinewa me karya kuma wanda bai ce amin ba Allah ya hada dashi. Ya bayyana hakane a wani wa'azinsa da ya watsu sosai. Malam ya soki Ministan sosai inda yace ba gaskiya bane abinda ministan ya fadi. https://www.tiktok.com/@ustazbabaa/video/7535964804993912120?_t=ZS-8yjmJor8CLw&_r=1
Gwamnan Kano ya sallami masu taimaka masa guda biyu

Gwamnan Kano ya sallami masu taimaka masa guda biyu

Duk Labarai
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sallamar masu taimaka masa guda biyu bisa laifuffuka daban-daban, sannan aka wanke guda ɗaya bayan kwamitocin bincike sun gabatar da rahoton binciken su. Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Musa Tank Muhammad ya fitar. Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da sallamar Abubakar Umar Sharada, babban mai taimaka wa gwamna kan tattara jama'a bayan kwamitin binciken ya gano shi ne ya kitsa yadda aka yi belin wanda ake zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Haka kuma gwamnan ya amince da sallamar Tasiu Al'amin Roba bayan kwamitin bincike ya tabbatar da hannunsa a kwana da kayan tallafin a rumbun gwamnati na Sharaɗa, wanda kuma tuni aka gabatar da shi a ...