Wednesday, April 1
Shadow

Duk Labarai

Gwamnan Katsina ya tafi hutu don kula da lafiyarsa

Gwamnan Katsina ya tafi hutu don kula da lafiyarsa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya sanar da tafiya hutun mako uku don kula da lafiyarsa. Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango ya fitar, ya ce gwamnan zai fara hutun ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agustan 2025. “Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi aiki cikin yanayi mai kyau, na ɗauki wannan matakin tafiya hutu, kuma zan dawo da zarar likitoci sun gama duba ni,'' in ji Gwamna Radda. Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Malam Faruk Jobe. A watan Yuli ne gwamna Radda ya yi hatsarin mota a kan hanyar Katsina zuwa Daura.
Yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dai-dai ta ƙarkashin Tinubu – Okonjo-Iweala

Yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dai-dai ta ƙarkashin Tinubu – Okonjo-Iweala

Duk Labarai
Yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dai-dai ta ƙarkashin Tinubu - Okonjo-Iweala. Darakta-Janar ta Hukumar kula da kasuwanci ta duniya WTO Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a ranar Alhamis ta gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inda ta yabawa gwamnatin Tinubu kan canje-canje da tayi domin dai-dai ta tattalin arzikin Najeriya. Okonjo-Iweala wadda ta bayyana ganawar da tayi a matsayin abinda taji daɗi, tace Shugaban Ƙasa ya nuna ya na son zantawa da'ita bayan tabi Uwargidan sa wajen ƙaddamar da kuɗaɗe ga mata. Kuɗaɗen wanda Hukumar kula da kasuwanci WTO da cibiyar kula da kasuwanci ta duniya ITC da ke Geneva suka samar, nada nufin haɓɓaka kasuwanci da samar da ayyukan yi da samar da kuɗaɗen shiga ga mata. Daga Usman Salisu
Gwamnatin tarayya ta turo munafuki cikin mu sannan hadi da matsin EFCC, zamu dan ja baya da maganar shirin kayar da Tinubu a zaben 2027>>Jam’iyyar ADC

Gwamnatin tarayya ta turo munafuki cikin mu sannan hadi da matsin EFCC, zamu dan ja baya da maganar shirin kayar da Tinubu a zaben 2027>>Jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar ADC na shirin ja da baya kan shirinta na kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa. Hakan na zuwane bayan da jam'iyyar ta gano cewa, Gwamnatin tarayya ta tura mata munafukai a cikinta da su rika kai mata bayanan sirri. Hakannan wannan na zuwane jim kadan bayan binciken da EFCC tawa Sanata Aminu Waziri Tambuwal wnda ake rade-radin zai wa wani da zai fito takarar shugaban kasa daga kudu mataimakin shugaban kasa .
Sai mun biya Naira Miliyan 3 ake yadda mu gabatar da kudirin doka a majalisa>>Inji Dan majalisar tarayya Hon. Ibrahim Usman Auyo

Sai mun biya Naira Miliyan 3 ake yadda mu gabatar da kudirin doka a majalisa>>Inji Dan majalisar tarayya Hon. Ibrahim Usman Auyo

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa, Hon. Ibrahim Usman Auyo ya yi zargin cewa sai sun biya tsakanin Naira Miliyan 1 zuwa 3 sannan ake yadda su gabatar da kudirin doka a majalisar tarayya har a karantashi a zauren majalisar. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta. Ya kara da cewa, bayan haka sai mutum ya bi 'yan majalisar yana rokonsu akan su goyi bayan kudirin nasa. Yace dan haka maganar gabatar da kudirin doka a majalisar ya zama hanyar samun kudi.
Ba gaskiya bane, Tùrji bàì tuba ya mika wuya ba>>Inji Sojojin Najeriya

Ba gaskiya bane, Tùrji bàì tuba ya mika wuya ba>>Inji Sojojin Najeriya

Duk Labarai
Sojojin Najeriya sun musanta ikirarin dake cewa gawurtaccen me garkuwa da mutane, Bello Turji ya tuba ya mika wuya. Me magana da yawun sojojin, Maj.-Gen. Markus Kangye ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis. Yace Bello Turji bai mika wuya ba har yansu suna bin sahunsa. Ana zargin Turji da hannu a garkuwa da mutane da kisa da sauransu.
Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara

Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami'o'i masu zaman kansu guda tara a faɗin Najeriya. Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan taron majalisar zartarswa ta ƙasa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja. Ya ce jami’o’in da aka amince da su sun haɗa da: Jami’ar Tazkiyah da ke jihar Kaduna Jami’ar Leadership da ke babbar birinin tarayya, Abuja Jami’ar Jimoh Babalola a jihar Kwara Jami’ar Bridget, Mbaise a jihar Imo Jami’ar Greenland da ke jihar Jigawa Jami’ar JEFAP a jihar Neja Jami’ar Azione Verde da ke jihar Imo Jami’ar Unique Open a Jihar Legas Jami’ar American Open da ke Jihar Ogun Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaji buƙatu 551 ...
Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil

Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil

Duk Labarai
Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil. Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyara zuwa ƙasashe biyu, Japan da Brazil a yau Alhamis, 14 ga watan Agusta. Bayo Onanuga, mashawarcin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya ce Tinubu zai tsaya a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kafin ya zarce zuwa Japan. Ana sa ran shugaban zai halarci taron ƙasa da ƙasa na tara kan ci gaban Afirka (TICAD9) a birnin Yokohama na ƙasar Japan daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta. Onanuga ya ce Tinubu zai kuma gudanar da tarukan tattaunawa tsakanin ƙasashe da kuma ganawa da shugabannin manyan kamfanonin Japan da ke da hannun jari a Najeriya. “Bayan kammala taron TICAD9, Shugaba Tinubu zai tafi birnin Brasilia, babban birnin Ƙasar Tarayyar Brazil, domin ziyar...
Kalli Bidiyon da Rahama Sadau ta wallafa da yasa ake ta tunanin Ko Ali Jita ne ta aura

Kalli Bidiyon da Rahama Sadau ta wallafa da yasa ake ta tunanin Ko Ali Jita ne ta aura

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta wallafa Bidiyon wakarta da Ali Jita a shafinta na sda zumunta bayan daura aurenta. Hakan yasa da yawa suka rika tunanin ko dai Ali Jita dinne ta aura? kalli Bidiyon anan Cece-kuce da kaguwar ganin waye Mijin Rahama Sadau ya karade kafafen sada zumunta inda aka rika yada hotunan mutane daban-daban ana cewa sune suka aureta.