Allah Sarki: Ji Yanda aka baiwa Buhari jirgin sama lokacin yana kan mulki amma yace baya so
Har Kyautar Jirgi Aka Yi Wa Marigayi Buhari A Lokacin Yana Kan Mulki, Amma Ya Ki Karba, Cewar Garba Shehu
Mai magana da yawun tsohon Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayar da labarin yadda marigayin ya ƙi karɓar wasu kyautuka lokacin yana mulki, ciki har dakyautar jirgin sama.
Da yake magana ta cikin shirin Inside Sources na Channels TV, Garba Shehu ya ce Buhari ya ƙi amincewa da karɓar kyautar agogon lu'ulu'u wani ɗankasuwa a Najeriya ya ƙera da sunansa a jiki, da kuma kyautar jirgin sama da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi masa tayi.
"Shugaban ƙasa ya kalli agogon, ya ce 'Agogon lu'ulu'u? Ba zan iya saka wannan ba. Ku faɗa masa yana ƙoƙari…kuma za mu ci gaba da ƙarfafa masa gwiwa. Ya ci gaba da ɗaukaka sunan Najeriya, amma ku mayar masa da agogon n...








