Sunday, April 5
Shadow

Duk Labarai

Ashe Kwankwaso bai samu ganin Shugaba Tinubu a zuwan da yayi Villa, Ji yanda ta kasance

Ashe Kwankwaso bai samu ganin Shugaba Tinubu a zuwan da yayi Villa, Ji yanda ta kasance

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbatar da cewa, zuwa na karshe da Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi zuwa fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai samu ganin shugaban kasar ba. An ruwaito cewa Kwankwaso da shugaba Tinubu sun gana ranar Litinin din data gabata. Saidai Rahoton Daily Trust yace ba'a yi ganawa tsakanin Tinubu da Kwankwaso ba. Daily Trust tace wani taro ne ya kai Kwankwaso fadar shugaban kasar amma ba ganawa da Tinubu ba. Daily Trust ta kara da cewa majiyoyi na kusa da shugaban kasar sun tabbatar mata da cewa babu wata ganawa da aka yi tsakanin shugaba Tinubu da Kwankwaso.
Ko da ‘yan Arewa basu yi Tinubu ba zai ci zaben 2027, saboda duka kudanci shi zasu zaba, kuri’a kadan yake nema daga Arewa ya ci zabe>>Inji Ayodele Fayose

Ko da ‘yan Arewa basu yi Tinubu ba zai ci zaben 2027, saboda duka kudanci shi zasu zaba, kuri’a kadan yake nema daga Arewa ya ci zabe>>Inji Ayodele Fayose

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa kudancin Najeriya gaba daya na Shugaba Tinubu ne. Yace Tinubu kuri'u kadan yake bukata daga Arewa ya ci zabe. Fayose ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace Peter Obi ne zai zo na 2 sannan sai jam'iyyar ADC zata zo na 3 sai watakila PDP ta zo na 4. Ya bayyana cewa idan aka lura da Tarihin da Tinubu ya kafa a siyasar Najeriya, da wuya ya fadi zaben 2027.
Ni shaida ne kaf Najeriya babu dan siyasar da ya kai Buhari Gaskiya da karamci>>Inji Sanara Henry Seriake

Ni shaida ne kaf Najeriya babu dan siyasar da ya kai Buhari Gaskiya da karamci>>Inji Sanara Henry Seriake

Duk Labarai
Tsohon gwannan jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari na da gaskiya inda yace babu wanda ya kaishi gaskiya a cikin 'yan siyasar Najeriya. Ya bayyana hakane a zauren majalisar Dattijai inda yace Buhari na da karamci da kima sosai. Ya bayar da labarin yanda Kotu ta tsige gwamnan APC a jihar Bayelsa kuma shugaba Buhari ya yadda da hukuncin ba tare da ja ba. https://twitter.com/ibhas1/status/1948624712407433390?t=m3THWd-jeuzOYYsvRk7gMw&s=19
Kalli Bidiyon da yasa aka kama Sultan me watsa labarai a Tiktok, An gurfanar dashi a gaban kotu inda aka zargeshi da cusawa ‘yan Najeriya kiyayyar shugaba Tinubu

Kalli Bidiyon da yasa aka kama Sultan me watsa labarai a Tiktok, An gurfanar dashi a gaban kotu inda aka zargeshi da cusawa ‘yan Najeriya kiyayyar shugaba Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Hukumar tsaro ta DSS ce suka kama matashi Sultan me watsa labarai a Tiktok daga gidansa inda suka wuce dashi Abuja. Asalin sunan Sultan shine Ghali Isma’il kuma a ranar Juma'a watau Jiya aka gurfanar dashi a gaban kotun Magistre dake Abuja bisa zargin yayi ikirarin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mutu. Sannan an zargeshi da cusawa 'yan Najeriya kiyayyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Dan haka alkalin kotun yasa aka tafi dashi zuwa gidan gyara hali na Keffi. Ismail dan shekaru 29 wanda dan asalin garin Jogana ne na karamar hukumar Gezawa jihar Kano. An zargeshi da cewa, yayi ikirarin samun bayanai cewa wai ahugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ci guba a abinci ya mutu. An zargeshi da dora Bidiyon a shafin Tiktok me sunan @bola_asiwaju...
Kalli Bidiyo: Buhari ya gama sukar Marigayi ‘Yar’adua amma shima gashi a Landan ya rigamu gidan gaskiya>>Inji Malam

Kalli Bidiyo: Buhari ya gama sukar Marigayi ‘Yar’adua amma shima gashi a Landan ya rigamu gidan gaskiya>>Inji Malam

Duk Labarai
Malam ya soki tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari kan yanda ya rasu a Landan. Yace haka lokacin 'yaradua ya rika sukarshi bayan ya rasu a Asibitin kasar Saudiyya kuma gidajen jaridu sun buga. Yace yana fatan Allah yawa shugaba Buhari Rahama amma maganar gaskiya abinda shuwagabannin Najeriya ke yi na kasa kula da bangaren lafiya bai kamata ba. https://www.tiktok.com/@sheik.lawan.trium/video/7531105454777339192?_t=ZM-8yLFWs7rgJx&_r=1
Bamu Yadda ba: Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya, ASUU za ta kai karar shugaba Tinubu Kotu saboda sakawa jami’ar UNIMAID dake Maiduguri sunan Muhammad Buhari

Bamu Yadda ba: Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya, ASUU za ta kai karar shugaba Tinubu Kotu saboda sakawa jami’ar UNIMAID dake Maiduguri sunan Muhammad Buhari

Duk Labarai
Kungiyar malaman Jami'a ta ASUU tace zata kai karar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kotu saboda sakawa jami'ar UNIMAID dake Maiduguri sunan tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari. Kungiyar tace ta cimma wannan matsaya ne bayan taron data gudanar wanda ya hada hadda wakilan kungiyar dalibai. Sanarwar bayan taron da aka fitar ranar Juma'a wadda ta samu amincewar shugaban kungiyar Abubakar Mshelia da mataimakin sakatare na kungiyar, Peter Teri tace basu amince da wannan mataki ba. Hakanan sanarwar tace an dauki wannan mataki ne ba tare da tuntubar ma'aikatan jami'ar da kungiyar ta ASUU ba da kuma kungiyar daliban da suka kammala makarantar a baya ba. Sanarwar tace canja sunan zai shafin tarihin da makarantar ta kafa na tsawon shekaru 50 da suka gabata. Dan haka ace ...
Kalli Bidiyo: Mai Shadda ma ya zubar da hawaye saboda Ummi Nuhu

Kalli Bidiyo: Mai Shadda ma ya zubar da hawaye saboda Ummi Nuhu

Duk Labarai
Ba zan iya tuna rabon da kwalla ta fito a idona sai jiya. Wallahi akwai rashin hankali sosai a cikin rayuwar nan. Yawancin matan da muke sakawa a film da kuma matan da suke ganin sun waye sosai, ko kuma gangar daukaka tana buga musu to Ina son suje su bibiyi rayuwa da tashen da UMMI NUHU tayi a harkar Kannywood da kuma Fagen Daukaka. Rayuwar “ya mace gajera ce, domin duk kyanki duk daukakarki ba zaki taba kai shekara ashirin da duka wadannan abubuwan ba. Ya Allah ka shiryemu, kasa muyi kyakkyawan karshe.Wasu daga cikin matan da suke ganin babu wanda ya isa ya basu shawara, ko kuma ya fadamusu GASKIYA please Kuje Shafin GABON TALK SHOW ku Kalli hirar da da UMMI NUHU, na tabbatar sai jikinki yayi sanyi. Allah ya shiryemu baki daya, Ameen summa Ameen. Kalli Bidiyon anan https:...
Kalli Bidiyo: Sanata Abdul Ningi ya zama sanata daya Tilo da yace bai yadda a baiwa Gwamnatin Tinubu damar ciwo bashin Dala Biliyan $21 saboda akwai rufa-rufa a lamarin

Kalli Bidiyo: Sanata Abdul Ningi ya zama sanata daya Tilo da yace bai yadda a baiwa Gwamnatin Tinubu damar ciwo bashin Dala Biliyan $21 saboda akwai rufa-rufa a lamarin

Duk Labarai
Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa bashin da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta aikewa da majalisar bukatar ciwoshi akwai matsala Yace babu cikakkun bayanai karara da suka fadi yanda za'a kashe kudin bashin da suka kai Dala Biliyan $21 komai an yi shi a dukunkunene. Saidai duk da wannan korafi na Sanata Ningi bai hana majalisar amincewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ciwo bshin ba. https://twitter.com/ArewaFactsZone/status/1948698363433812057?t=5IVqsMrpMxG7niOUkzijSw&s=19
Kalli Bidiyo: Dansandan Najeriya ya koka da bashi Naira Miliyan 2.8 a matsayin kudin sallama bayan kammala aikin da ya shafe tsawon shekaru 35 yana yi, yace wannan rashin adalci be ba zai karbaba

Wani tsohon dansandan Najeriya da yayi ritaya aka bashi Naira Miliyan 2.8 a matsayin kudin Sallama yace ba zai karbaba. A bidiyonsa da aka gani yana jawabi yace ya shafe shekaru 35 yana aiki amma a bashi Naira Miliyan 2.8 a matsayin kudin sallama, yace wannan cin fuska ne. Yayi kira ga shugaban 'yansanda da ya shiga lamarin. https://twitter.com/SaharaReporters/status/1948867610335941109?t=RtUE1n8GUawT5YULtv8BnA&s=19