Matashiyar nan marar kunya ta jihar Legas, Ayomiposi Oluwadahunsi wadda aka fi sani da Mandy Kiss tace duk da kundin tarihin Duniya yace ba zai karrama ta ba idan ta yi lalata da maza 100, ba zata fasa ba.
Tace tuni ta sayi fakiti na kwandam inda take gayyatar maza zuwa Ikorodu.
Tace ko da mutum ba zai yi ba, tana gayyatarsa ya je ya sha kallo.
Ta bayyana cewa dai a watan Oktoba ne zata aikata wannan masha'a saidai bata fadi sunan wajan da zata aikata hakan ba.
https://twitter.com/Teeniiola/status/1970723550521893060?t=_QdTAUIMpixvtqGHkHOeLA&s=19
https://twitter.com/Teeniiola/status/1971143834601132165?t=1bukeNydE-hM6KU_yjWQ1g&s=19
Rahotanni sun ce har yanzu gidajen man fetur na sayar da man a farashi me tsada duk da rage farashin da matatar man fetur ta Dangote ta yi.
A makon daya gabata ne Matatar man ta sanar da rage farashin daga Naita 865 zuwa naira 820 akan kowace lita musamman tace saboda tankokin man ta 1000 zasu fara jigilar man zuwa gidajen mai kyauta.
Saidai binciken da jaridar Punchng ta yi yace har yanzu a jihohin Legas da Ogun da sauran wasu jihohi gidajen man basu fara sayar da man a sabon farashi ba.
Tauraruwar Tiktok, Rahama Sa'idu ta bayyana cewa, Wannan jakar farashinta Naira 105,000 ne a shagonta.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyonta da ya karade kafafen sadarwa inda lamarin ya baiwa mutane mamaki musamman kanin jikar karamace sosai.
Kalli Bidiyon anan
Wannan amaryar daga jihar Bauchi me suna shahida Sani ta amince da Qur'ani a matsayin sadakinta maimakok kudi da aka saba bayarwa.
An daura aurenta da angonta, Aliyu Haidar ranar Asabar data gabata a unguwar Saleh Saleh dake jihar Bauchi.
Lamarin ya dauki hankula inda akaita muhawa da kuma yabawa saukin kan amaryar
Rahotanni sun bayyana cewa, Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka aikawa matar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Watau Remi Tinubu da tallafin data nema na zagayowar ranar Haihuwarta.
Remi Tinubu ta nemi a tara mata kudi a yayin data cika shekaru 65 da haihuwa inda tace za'a yi amfani da kudin wajan kammala ginin hedikwatar dakin karatu na kasa.
Tuni aka sanar cewa kudin sun kai sama da Naira Biliyan 20 wadanda 'yan Najeriya suka tara mata.
Saidai wani abin mamaki shine, cikin jerin mutanen da suka tura mata da kudaden tallafin hadda tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.
Hakan na zuwane duk da cewa, tun kamin Uwargidan shugaban kasar ta fara neman wannan tallafin Buhari ya rasu.
Abin ya zowa mutane da yawa da mamaki matuka.
...
A'isha Beauty ta bayyana cewa, Gidan iyaye yafi dadi.
Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace masu zaginsu, su da suka baro gidan iyayensu suka shiga bariki su daina.
Ta yi rokon a rika musu addu'ar Allah ya shiryesu.
Ta kuma yiwa masu shirin barin gidan iyayensu su shiga bariki addu'ar Allah ya karkatar da zuciyarsu zuwa daidai.
https://www.tiktok.com/@aysha.beauty50/video/7553099428987555080?_t=ZS-901OilwIYxF&_r=1
Shahararren me kudi a jihar Delta, Jim Brown ya auri mata ta 19.
Wani karin abin daukar hankali shine wasu daga cikin sauran matan nasa sun halarci wajan bikin.
Lamarin ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda akai ta muhawara.
Wannan wani me hakar Kabari ne da ya bayar da labarin irin ni'imar da ya taba gani a cikin wani kabari.
Yace yana hakar sabon kabari ne shine kafarsa ya zurma cikin wani kabari, yace kawai sai yaji wata irin ni'ima har cinyarsa.
https://www.tiktok.com/@g_fresh_alameen0/video/7553053843660082444?_t=ZS-901B0WxBJj7&_r=1
Ya kuma bayar da labarin wasu kaburburan da yace sai kasusuwa ake gani.
Rahotanni daga hukumar kula da harkar man fetur a Najeriya, watau Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission, sun ce an sace jimullar danyen man fetur na Naira Tiriliyan N8.41tn.
Rahoton yace an yi wannan gagarumar satar ne a tsakanin shekarun 2021 da 2025.
Saidai rahoton yace a yanzu an samu raguwar satar danyen man ba irin a baya ba amma duk da haka jimullar yawan danyen man da aka sace ya nuna gazawar gwammati.
Me sharhi akan Almuran yau da kullun, Professor Ayoade yace abin takaici ne ace an tafka irin wannan asarar amma babu wanda aka hukunta.