Yanda ‘yansanda suka min fàdè a bakin boda>>Wata ‘yar Najeriya data je cirani kasar Libya ta dawo da kyar ta bayar da labari
Wata 'yar Najeriya data je Cirani kasar Libya ta dawo da kyar ta bayar da labarin irin wahalar data sha.
Matar sunanta Olaonipekun Adenike kuma shekarunta 30 tana da 'ya'ya 2.
Tace ita kadai ce a wajen mahaifiyarta dan duk 'yan uwanta sun mutu.
Tace ta so yin karatu har ta fara amma rashin kudi yasa dole ta hakura.
Tace ta hadu da wata kawar mahaifiyarta a facebook wadda take zaune a kasar Libya wadda ta tambayeta abinda take yi inda ta zayyana mata komai, tace daga nan ne sai kawai magaifiyartata tace mata zata taimaketa musamman saboda irin kirkin da mahaifiyarta ta mata lokacin suna tare.
Tace ta shirya ta je Libya aikatau. Tace ta ji dadin hakan inda suka tashi daga garinsu, Sagamu dake jihar Ogun suka tafi Libya.
Tace sun je Legas suka je Kano suka shiga Nijar, tace ...








